Hukumar samar da agajin gaggauta ta jihar Adamawa (ADSEMA) ta shaida cewar ambaliyar ruwa ta ci rayukan mutum hudu yayin da uku suka gamu da munanan raunuka a cikin kauyuka tara da ke karamar hukumar Madagali a jihar.
Sakataren hukumar ADSEMA mai cikakken iko, Dakta Suleiman Adamu Muhammad, ya kuma ce mutum 8,400 ne ambaliyar ta sha yayin da kuma mutum 5,352 ke zaman gudun hijira a makarantar Firamare ta Lumadu Shuwa yayin da wasu kuma ke zaune a gidajen makusantansu.
Muhammad ya shaida wa LEADERSHIP a garin Yola cewa, ambaliyar ta rusa gidaje da dama, ya kara da cewa ana kokarin samar da kayan tallafin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa a wuraren da suka yi kaura.
Ya daura da cewa kadarori na biliyoyin naira me suka lalace sakamakon wannan ambaliyar.
Ya kara da cewa an fara raba ma wadanda lamarin ya shafa kayan agaji da tallafin a kauyukan da ambaliyar ta shafa Shuwa, Gulak, Sabon Gari, Hyumbula, Vapura, Palam, Mayo-Wandu, Wuro-Ngayandi da kuma Kirchinga.
Daga bisani ya shawarci wadanda suke zaune a wuraren da ruwa ke bi domin kauce wa barnar da ruwa ke yi.