Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na yin hawan Sallah don kauce wa tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan damuwa kan yiwuwar samun rikici, bayan da sarakunan biyu, Muhammadu Sanusi II, da Aminu Ado Bayero suka shirya gudanar da bukukuwan hawan Sallah daban-daban.
- Mahukuntan Lai Ching-te Sun Salwantar Da Muradun Kasa Wajen Neman ’Yancin Kai Bisa Dogaro Da ’Yan Katsalandan Na Ketare
- Boko Haram Ta Kashe Sojoji A Wani Sabon Hari A Borno
A jawabin da ya yi a ranar Laraba da daddare, Aminu Ado ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan tuntuɓar malamai, dattawa, da mambobin majalisarsa.
“Hawan Sallah ba wajibi ba ne. Idan zai haifar da tashin hankali ko asarar rayuka, gara a soke shi,” in ji shi.
Ya buƙaci jama’a su mayar da hankali kan dangantaka da zumunci a lokacin bukukuwan Sallah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp