Shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya kwashe watanni shida yana mulki a kasarsa. Ayyukan da ya yi a wadannan watanni sun bayyanawa kasashen Afirka karara cewa, Afirka ba ta cikin jerin fannoni da kasar Amurka ta baiwa fifiko.
Idan aka kwatanta da wa’adin shugaba Trump na farko, wanda ya kunshi yadda ya yi wa kasashen Afirka wulakanci ta hanyar kiransu da lakabai marasa dadin ji, da rashin kulawa da ya nuna wa nahiyar (ya gana da shugabannin kasashen Afirka biyu kadai, kuma bai taba ziyartar Afirka ba), shugaba Trump ya kara daukar matakai kan Afirka a wa’adinsa na biyu.
- Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
- 2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC
Misali, ya rufe Hukumar Raya Kasashen Duniya ta Amurka (USAID), tare da rage yawan tallafin da kasar take baiwa Afirka. Ya kuma bayyana shirinsa na soke shirin kasarsa na tallafawa kokarin yaki da cutar kanjamau a duniya (PEPFAR), duk da cewa lamarin zai iya haddasa asarar miliyoyin rayuka a Afirka.
Kazalika, manufar karbar karin harajin fito da shugaba Trump ya kaddamar za ta karawa kasashen Afirka nauyi sosai. Kana wani umurnin da ya saka masa hannu a baya-bayan nan shi ne takaita damar ‘yan kasashen Afirka bakwai, ciki har da Najeriya da Kamaru, ta fuskar bizar zuwa Amurka.
Afirka ta Kudu yana daya daga cikin kasashen Afirka da suka fuskanci matsin lamba na musamman daga Shugaba Trump: Amurka ta kori jakadanta, kuma manyan jami’an kasar Amurka sun kaucewa dukkan taruka masu alaka da G20, da Afirka ta Kudu ta karbi bakunci. Ban da haka, ganawar da shugaba Trump ya yi da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ma ta rikide, har ta zama tamkar cacar baka a wani lokaci. Abubuwan da aka yi tababa a kai sun hada da zargin da Amurka din ta yi wa Afirka ta Kudu, cewa wai tana yi wa al’ummarta ‘yan asalin Turai “kisan kiyashi”, da yadda Afirka ta Kudu ta kasance mamba a kungiyar BRICS, da kuma yadda kasar ke dora muhimmanci kan batun sauyin yanayi a lokacin da take shugabancin kungiyar G20.
Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu kasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alakar tarihi tsakanin kasar Laberiya da Amurka. Bugu da kari, Trump ya katse maganar shugaban kasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar—ba domin neman karfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka din damar samun ma’adanan da take bukata, da yiwuwar sanya wadannan kasashen dake nahiyar Afirka amincewa da karbar bakin haure da ake korarsu daga Amurka.
Watakila, shugaba Trump ba ya mai da hankali sosai kan da’a a fannin diflomasiyya, amma idan aka kwatanta da shugabannin kasar Amurka da suka gabace shi, to, a kalla yana bayyana kome a fili ba tare da rufa-rufa ba. Maganarsa da matakan da ya dauka, dukkansu na isar da sako zuwa ga kasashen Afirka cewa: “Ba ku cikin jerin fannonin da Amurka take nunawa fifiko.” “Za mu iya musayar wasu abubuwa, amma kada ku yi tsammanin za ku samu riba ko alfanu sosai.” (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp