An Bankado Wasu Jami’an Tsaro Na Ba Da Umarnin Kotu A Bayan Fage

Dan Kasuwa

Daga Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki,

Sakamakon kutsen da aka yi a gidan Mai Shari’a Mary Ukaego Odili ta kotun koli domin binciken kwakwaf da wasu jami’an tsaron da har yanzu ba a iya gano ko su waye ba suka yi yunkurin yi, Jaridar LEADERSHIP ta gano cewa, wasu daga cikin jami’an gwamnati na mallakar takardun umarnin kotu da suke cikewa da kansu don cafke wadanda suka ga dama.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da wakilinmu cewa, abin da ya faru a gidan mai shari’a Mary Ukaego Odili, a makon da ya gabata, bai kamata a danganta shi da umarnin da kotu ta bayar ba, don haka abin da ya faru daban, umarnin kotu kuma daban.

Idan za a iya tunawa dai, an wayi gari da ganin jami’an tsaro jibge a gidan mai shari’a Maryam Ukaego, wadanda aka nuna sun je gidan ne domin su gudanar da bincike, wanda aka bayar da  takardar sanarwar  gudanar da shi a ranar 20 ga watan Oktoba, 2021.

Yanzu haka za a iya cewa, kallo ya koma sama, domin kuwa ana zargin, ofishin babban mai shari’a na kasa da Hukumar  EFCC da kuma jami’an tsaro na farin kaya wato, DSS, wadanda dukkansu sun ki cewa komai dangane da wannan rahoto da aka bayar.

Dattawan da ke da ruwa da tsaki a kan harkar shari’a a kasar nan, sun soki lamarin wannan tataburzar da ake yi a wannan bangare na shari’a domin kamar yadda suka ce, ba zai haifarwa da kasar nan da mai ido ba, a bangaren shari’a, domin bangare ne da ke da matukar muhimmanci, don haka bai kamata a dinga samun irin wannan rashin fahimta ba.

Haka kuma binciken da aka gudanar ya gano cewa, wasu ma’aikatan kotuna suna kawo cikas wajen bayar da dama ga masu kara su bayyana gaban alkalin domin yi wa kotu bayani yadda alkali zai fahimce su, wanda kuma ta hanyar hakan ne kawai za a iya tabbatar da dalci. Maimakon haka sai su kafa shinge tsakanin masu shari da wadanda aka gurfanar gaban kotu.

Majiya mai tushe ta bayyana wa jaridarmu cewa, wani lokaci ma ‘yansanda kan karbi takardar kotu wadda ba a cika ba, a hannun wasu kanan kotuna, domin su yi amfani da ita a matsayin barazanar gurfanar da mutum gaban alkali, wanda yin hakan na jefa wasu mutane da dama cikin damuwa. Daga irin haka ne wasu ke tsorata su bukaci a yi sulhu tun kafin a kai ga gurfanar da su gaban alkali, saboda haka, wannan na daga cikin irin manyan kalubalen da suka dabaibaye harkar shari’a har ta tsinci kanta a wannan hali na gaba kura baya siyaki.

Wata kungiya mai fafutukar tabbatar da adalci a bangaren siyasa da shugabanci ta bakin shugabanta Momodu Tarka, ta ce irin wannan badakala da ke faruwa a bangaren shari’a na da nasaba da kutsen da aka yi wa Mai Shari’a Odili kuma akwai alaka mai karfi da rikicin shugabancin da ya sharke Jam’iyyar PDP kafin gudanar da babban taronta na kasa a makon jiya.

Sai kuma wani hanzari ba gudu ba, Babban mai shari’a na kasa  Abubakar Malami SAN, ya nuna cewa, babu umarninsa wajen wannan tada kura da ake yi a sashin shari’ar.

Exit mobile version