Mawakan arewa sun kafa wata sabuwar kungiya da suka yi wa sunan tatin-tatin (13×13) domin taimaka wa sassan ci gaban al’umma.
A cikin wata sanarwa daga sakataren kungiyar, Hashim Abdallah, an bayyana cewa, “Kungiya ce da mutum 13 suka samar da ita kuma alkhairi ce ga al’umma kamar yadda taken tafiyar yake, da aka yi imani zai ‘yanta ‘yan Nijeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko wakar siyasa ko kamfe. Ba ta da wani makiyi sai makiyin al’umma. A dalilin hadafi na ‘yanta kasa, lallai 13×13 ta kafu ne mahadi-ka-ture wato har illa mashaAllahu.
“Wannan yunkuri ne da manufar dago da masu fasaha da masu baiwa, daga mawaka, marubuta jaruman fim, ‘yan wasan kwaikwayo ko dago da darajar wadannan masu fasaha a kowane fage na basirar da Allah Ya ba su a siyasa ko waken al’uma ko wa’azi ko don harshe wato adabi a dunkule. Yunkurin na da manufar nuna kimarsu ko irin rawar da suke takawa ko za suke takawa fiye da gaban a aikin fasahar ko bayan wannan baiwa, abubuwan da suka hada da neman cigaban al’uma kuma domin tallafa wa al’umar da ciyar da ita gaba, bisa jagorancin manyan mawaka da sauran masu fasaha da basira da kafatanin masu ruwa da tsaki a wannan fagage da aka ambato. Tafiyar harkar nau’ukan adabi domin adibai da janibinsa.
“Yana da muhimmanci mu fahimci tafiyar ba ta siyasa ba ce, kuma za a iya cewa tafiyar ta siyasa din ce domin akwai tunanin ceto kasar da fafutukar samuwar shugabanni nagari a kowacce jam’iyya kuma bisa yarjejeniya da fafutukar talakawa da yarjewarsu domin ake cika musu alkawari da samar da shugabanni nagari, domin wayar da su domin wayar da su kan manufofin nusar da su muhimmanci irin nasu, a matsayin gudumawar mawaka.
Wannan kungiya tana da shugabanci mataki-mataki, kuma shugaba na kasa shi ne, Dauda Kahutu Rarara da Kwamitin gudanarwar jihohi na kasa karkashin babban mawaki ElMu’az Birniwa. Babban marubucin fina-finai Ibrahim Birniwa ya kasance shi ne mataimakin shugaban kwamitin siyasa na kasa da sauransu.” In ji sanarwar.