An kaddamar da babban titin Mbour zuwa Kaolack da wani kamfanin gine-ginen tituna da gadoji na kasar Sin ya gina, yayin wani biki da aka yi jiya Asabar, a birnin Thiadiaye na yankin Mbour dake lardin Thies na yammacin Senegal.
Shugban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya halarci bikin, inda ya bayyana titin a matsayin alamar ingantacciyar dangantakar da ke tsakanin Senegal da Sin. Ya kara da cewa, titin na da matukar muhimmanci wajen saukaka zirga-zirga a yankin tsakiyar kasar da inganta hada yankin tsakiyar da sauran sassan kasar.
Ya ce yanzu za a iya amfani da titin wanda a baya aka tsara budewa a watan Satumba.Bugu da kari, shugaban ya gode wa kasar Sin bisa goyon bayan da take ba kasarsa, inda ya ce a shirye yake ya ci gaba da zurfafa dangantaka a tsakaninsu da ma daukaka hadin gwiwa da Sin.
Babban titin mai tsawon kilomita 99.2 ya hada birnin Mbour da ke gabar ruwa da kuma Kaolack dake yankin tsakiyar Senegal. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














