Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a Nijeriya, inda ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalolin.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna, inda ya nemi ’yan Nijeriya su sake zaɓensa a shekarar 2027.
Shugaban ƙasar ya kare manufofin tattalin arziƙin gwamnatinsa, tare da yin alƙawarin inganta rayuwar jama’a, bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ƙarin damarmaki idan aka sake zaɓensa.
Ya kuma yaba wa gwamnonin APC bisa ayyukan raya jihohinsu da kuma biyan albashin ma’aikata a kan lokaci.
Tinubu ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan masu zaɓe domin su zaɓi ’yan takarar APC a babban zaɓen 2027.
Ya ce batun cire tallafin man fetur ya zama tarihi, tare da yin alƙawarin samar da kyakkyawar makoma ga matasan Nijeriya.














