Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da wata takarda da ke yawo a shafukan sada zumunta wadda ke iƙirarin cewa Gwamna Uba Sani ya amince tare da fitar da kuɗi har Naira tiriliyan 2.3 domin ɗaukar nauyin taron buɗe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC, inda ta bayyana ta a matsayin ƙirƙirarriyar takardar bogi da nufin yaudarar mutane.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2026, a birnin Kaduna.
Maiyaki ya bayyana cewa takardar mai kwanan watan 18 ga Oktoba, 2026, mai taken “Notification for Preparations for the Grand Rally Flag Off” wadda aka yi ikirarin an aike wa Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC (APC-PCC), Sanata Abdul’aziz Yari, ƙazafi ne tsagwaronsa da ke ɗauke da ƙarairayi masu cin karo da juna.
Kwamishinan ya jaddada cewa gaba ɗayan kasafin kuɗin Jihar Kaduna na wannan shekara ta 2026 Naira biliyan 985.92 ne kacal, don haka iƙirarin cewa an fitar da Naira tiriliyan 2.3 ya ninka dukkan kasafin kuɗin jihar na shekara fiye da sau biyu, lamarin da lissafi da hankali ba za su taɓa ɗauka ba. Ya ƙara da cewa babu wani tanadi a kasafin kuɗi, ko amincewa, ko bayanan banki da ke nuna an fitar da irin wannan maƙudan kuɗaɗe.
Maiyaki ya kuma bayyana kura-kuran da ke jikin takardar da ke tabbatar da cewa ta jabu ce, ciki har da kuskuren rubuta sunan gwamnan a matsayin “Uba Sai” maimakon “Uba Sani”, gami da kwaikwayon sa hannun gwamnan ta hanyar da ba ta dace ba. Ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani bai taɓa rubuta ko ba da izinin rubuta wannan wasiƙa ba, kuma gwamnati ba ta ware ko fitar da ko kwabo daga irin wannan adadi ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa tun bayan karɓar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Gwamna Uba Sani ya sanya kyakkyawan tsarin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, gaskiya, da riƙon amana a gaba, tare da mayar da hankali wajen zuba jari a fannonin tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da noma.
Gwamnatin ta gargaɗi cewa ƙirƙirar takardun bogi na hukuma babban laifi ne a ƙarƙashin doka, inda ta buƙaci hukumomin tsaro da na bincike da su binciko tushen wannan takarda domin gurfanar da waɗanda ke da hannu a gaban kuliya, tare da yin kira ga kafafen yaɗa labarai da al’umma da su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su.














