An kama mutum 23 da ake tuhuma da aikata ayyukan zamba da yaudara ta amfani da hanyar sadarwa ta intanet, wanda hakan na nuna yadda wannan dabi’ar ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar nan.
Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa ta EFCC ta ce ta kama wasu mutum 23 da take tuhuma da ayyukan zamba ta amfani da kafar sadarwa ta intanet a Sakkwato.
Mutanen da ta kama da suka kasance daga manyan kabilun Nijeriya, an lura da yadda suke bushasha da kudi abin da ya saba wa hankali, don haka ya sa hukumar ta yi musu dirar mikiya ta kama su, kuma tana kan bincikensu, kafin ta gurfanar da su gaban kuliya idan ta same su da laifi.
Masanin sadarwar yanar intanet kuma babban sakatare na ma’aikatar da ke kula da fasahar sadarwar zamani a Sakkwato Nasir Daniya ya ce laifukan da ake aikatawa ta hanyar intanet suna da yawa kuma su kan zo ta sigogi mabambanta.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka kama masu wannan dabi’ar a Nijeriya musamman a Kudancin kasar abin da jama’a ke ganin yana da kyau mahukunta su kara tashi tsaye wajen maganin matsalolin.