An Cafke Wani Dan Fashi Sanye Da Kayan ‘Civil Defence’

’Yan sanda na reshen jihar Ogun sun samu nasarar cafke wani da ake zargi da fashi da makami mai suna, Adeolu Bankole na Idagba Kuarters, Ayetoro da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu ta jihar Ogun, wanda yawanci yake aikata mummunan aikin sa sanye da kayan jami’an tsaro na farin kaya (NSCDC).

A cewar sanarwar daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi a ranar Litinin, an ce, an kama Adeolu Bankole ne a ranar 5 ga watan Fabrairun 2021 biyo bayan korafin da wasu daliban jami’ar Olabisi Onabanjo, Ayetoro Campus suka yi.

An ce daliban sun kai rahoto ne a yankin da ke yankin Ayetoro cewa, wani dan fashi da makami ne ya yi awon gaba da kayansu ta hanyar nuna masu bindiga, wanda ya kutsa kai cikin gidansu, sanye da kayan jami’an tsaron farar hula ya kuma kwace musu wayoyinsu da kwamfutar tafi-da-gidanka.

Bayan rahoton, Kwamandan yankin, Ayetoro, ACP Anthony Haruna, ya ce, ya yi wa masu bincikensa cikakken bayani don su bi bayan dan fshin, inda suka shafe awanni suna gudanar da bincike, masu binciken sun samu labarin mabuyar wanda ake zargin.

Sanarwar kara da cewa, a lokacin da aka isa maboyar wanda ake zargin dan fashi da makamin ne, an samu wata jaka dauke da wayoyi shida, kwamfutar tafi-da-gidanka guda daya, rigar tsaro ta farin kaya da karamar bindiga.

Bayan wannan binciken, an ce masu binciken sun sanya ido a yankin kuma da misalin karfe 5 na yamma, wanda ake zargin ya shiga cikin ginin da ba a kammala ba wanda nan ne maboyarsa, sannan ya mike kai tsaye zuwa inda yake ajiye jakar, wnada hakan ya sanya aka jami’ai cafke shi nan take. An kuma gano wasu wayoyi biyu da aka sata da agogon hannu.

‘Yan sanda sun ce daliban jami’ar Olabisi Onabanjo, Ayetoro Campus da suka kawo rahoton faruwar lamarin dukkansu sun shaida wanda ake zargin a matsayin wanda ya yi musu fashin.

Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa, binciken ya kuma gano cewa wanda ake zargin ya saci jami’am tsaron farar hula a wata mota kirar Toyota mallakar wani jami’in NSCDC a watan Disambar 2020 sannan daga baya ya bankawa motar wuta. An ce, jami’in ya kuma gano kakin a matsayin nasa.

A halin yanzu, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Edward A. Ajogun ya ba da umarnin a tura wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin gudanar da bincike cikin tsanaki da kuma hukunta masu laifi.

Exit mobile version