Hotunan wani katon kinkimemen dutse na da aka cire daga mafitsarar wata budurwa kwanan nan ta hanyar tiyata yana ta zagaye a shafukan sada zumunta na Betinam.
Yawancin kafofin watsa labarai na Betinam sun ba da rahoto game da batun wata mace mai shekaru 34 da ta bayyana a dakin gaggawa na babban Asibitin Phu Binh, a Thay Nguyen, tana korafin fama da tsananin ciwo a ciki. Bayan gudanar da wasu gwaje-gwaje, wani hoton na ‘CT’ ya nuna cewa matar tana da wani katon dutse a cikin ta, wanda nan-da-nan aka tsara ta don yin aikin tiyata na gaggawa, kuma an samu nasarar fitar da dutsen wanda tsayinsa ya kai mita 10, kuma mai nauyin kusan giram 400.
Rahotannin labarai ba su bayar da bayanai da yawa game da wannan lamarin ba, amma hotuna ‘CT’ din na ta yawa a kafafen sada zumunta, yana nuni da wani katon dutse. Wannan lamari ya kasance bakon abu ne a asibiti.
Hotunan dutsen wanda nauyinsa ya kai giram 400 na mafitsarar macen mai shekara 34 ya bazu a cikin kasar Betinam a ‘yan kwanakin nan, tare da yawancin masu amfani da kafefen sda zumunta suna nuna rashin tausaya wa ga azabar da matar ta fuskanta kafin cire dutsen