Alkalin wat kotun gunduma ta daya da ke yankin Dei-Dei a Abuja, Malam Saminu Suleiman ya yanke wa wani dan kamasho, Godstime Iyere daurin hukuncin wata shida a gidan gyaran hali, ko kuma ya biya tarar Naira 30,000.
Iyere mai shekara 33 wanda yake zaune a unguwar Dankogi Zuba a Abuja, alkalin ya yanke masa hukuncin ne kan satar batirin mota, inda alkalin ya gargade shi da ya guje wa aikata wani laifi a nan gaba bayan hukuncin da kotun ta yanke masa.
- Wajibi Ne A Gudanar Da Bincike Na Gaskiya Game Da Lamarin Bututun “Nord Stream”
- Zabe: CBN Ya Musanta Shirin Katse Hada-Hadar Kudi Ta Intanet
Tun a farko, Iyere ya amsa laifin tuhumar da kotun ta yi masa, inda ya roki a yi masa sassauci.
Dan sanda mai gabatar da karar, Chinedu Ogada ya shaida wa kotun cewa, Iyere ya aikata wannan laifin ne a ranar 12 ga watan Janairu 2023, inda
ya sanar da cewa, laifin ya saba wa sashe na 287 final kod.
Ya kara da cewa, wani mai suna Ebere Opara da ke Abuja, ya shigar da korafi a caji ofis din ‘yansanda na Zuba a ranar 14 ga watan Fabirairu cewar an sace masa batirin mota an kuma sayar da shi kan Naira 30,000.
A cewar Chinedu, bayan ‘yansanda sun gudanar da bincike, Iyere ya amsa laifinsa.