Gwamnatin Jihar Taraba ta ƙaddamar da wani shiri na rigakafin cutar ƙyanda wanda ke da nufin kai wa ga yara kimanin miliyan 1.6 masu shekaru tsakanin wata tara zuwa shekara 14 a faɗin jihar.
A cewar gwamnati, wannan aikin zai gudana na tsawon kwanaki 10, inda za a riƙa yi wa yara ƴan ƙasa da shekaru biyar allurar cutar shan inna, sannan ‘yan mata masu shekaru tara za su karɓi rigakafin HPV wadda ke hana cutar sankarar mahaifa.
- Sojoji Sun Tarwatsa Maɓoyar ‘Yan Bindiga 11, Sun Ƙwato Makamai A Taraba
- Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Taraba, Kebbi Da Filato
Uwargidan gwamnan jihar Taraba, Hajiya Agyin Agbu Kefas, wacce ta jagoranci ƙaddamar da shirin a Jalingo, ta buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar babu wani yaro da aka bari a baya wajen yin rigakafin. Ta bayyana cewa gwamnati na da niyyar kare lafiyar yara daga waɗannan cututtuka masu saurin yaɗuwa.
Ta yi kira ga ma’aikatan lafiya, da abokan cigaba da shugabannin al’umma da su haɗa kai wajen tabbatar da nasarar wannan shiri, tana mai jaddada cewa rigakafi hanya ce mafi inganci wajen tabbatar da lafiyar yara a jihar.
A nasa jawabin, Sakatare na Hukumar Kula da lafiyar a matakin farko ta jihar, Dr. Nuhu Tukura, ya bayyana cututtukan masassara da rubella a matsayin barazana ga lafiyar yara a Nijeriya, yana mai cewa za a iya magance su ta hanyar yin rigakafi da wuri da kuma faɗaɗa yawan waɗanda suka samu. Ya ƙara da cewa ana sa ran wannan yunƙuri zai taimaka wajen rage yaɗuwar cututtuka da ake iya kaucewa ta hanyar rigakafi a jihar.














