A ranar Asabar masu binciken a karkashin teku sun gano wani jirgin fasinjan Japan na lokacin yakin duniya na 2, wato Montevideo Maru, wanda aka nutsar da shi a tekun Philippines dauke da ‘yan Australia 1000.
Sojin ruwan Amurka ne suka nutsar da wannan jirgi mai suna Montevideo Maru, mallakin Japan a shekarar 1941.
- Nijeriya Na Bukatar Addu’ar Al’umma Kan Zaman Lafiya – Dan Kaden Rano
- Har Yanzu Wasu Na Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Mutanen Banza —Auwal West
Jirgin ruwan yakin Amurka, wanda ma’aikatansa ba su ankare cewa jirgin na dauke da fursunonin yaki ne ya nutsar da wannan jirgi a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1942.
Kungiyar binciken tarihi na karkashin ruwa ta Silentworld, waddda ta dauki nauyin binciken ta ce an gano jirgin ne a waje mai nisan sama da kilomita 4 a karkashin tekun.
Nutsewar jirgin ruwan Montevideo Maru shi ne hatsarin jirgin ruwa mafi muni da kasar Australia ta fuskanta, inda ta yi asarar akalla mutane 979, cikinsu sojoji 850.
Fararen hula daga kasashe 13 na cikin wannan jirgi, abin daya kawo adadin fursunonin da suka mutu a cikinn1060.
Dakarun Japan ne suka kama su watannin baya kafin balaguron a garin gabar teku na Rabaaul a Papua New Guinea.
Bayan shafe shekaru 5 suna shiri, masu binciken sun fara aikin neman jirgin ne a ranar 6 ga watan Afrilu daga tekun kudancin China, Arewa Maso Yammacin tsibirin Luzon na Philippines.
Sun fara hangen nasara ne kwanaki 12 kacal bayan da suka kaddamar da neman jirgin ruwan, ta wajen amfani da na’urorin zamani har da motar karkashin ruwa.