Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo a gaban kotu kan zargin aikata laifukan ta’addanci.
An gurfanar da Bodejo a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja kan zarginsa da kafa da kuma tallafa wa kungiyar ‘yan bindiga ta ‘Kungiya Zaman Lafiya’ ba bisa ka’ida ba.
- ‘Yansanda Sun Kama Shugaban Kungiyar Miyetti-Allah A Adamawa
- Ba Mu Kama Shugaban Miyetti Allah Ba – DSS
An gurfanar da Bodejo ne a ranar Juma’a a kan tuhume-tuhume guda uku da ofishin babban mai shari’a na kasa ya shigar, inda ake tuhumarsa da karya dokar ta’addanci ta shekarar 2022.
Bodejo ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da ake yi masa a lokacin da aka karanto masa tuhumar a gaban kotu, daga nan ne mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar leken asiri ta DIA.
Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 27 ga watan Mayun 2024.
Idan za ku tuna kwanakin bayan an kama shugaban na Miyetti Allah a jihar Nasarawa, bayan kungiyar ta kaddamar da wata kungiyar ‘yan banga mai suna Kungiyar Zaman Lafiya.
A lokacin bikin kaddamar da kayan Fulani na mutum 1,144 a ranar 17 ga watan Junairu, 2024, Bodejo ya ce, an dauki wannan matakin ne don magance matsalar ‘yan fashi da satar shanu da ma duk wani nau’in rashin tsaro da yake addabar jihar Nasarawa.
Bayan kama shi, shugaban na Miyetti Allah, ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin kalubalantar tsare shi da aka yi.
A martanin da babban Lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), a ranar 5 ga watan Fabrairu, ya shigar da kara a gaban kotu, inda ya bukaci a ci gaba da tsare Bodejo har sai an kammala bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ke sauraron karar Bodejo, ya bai wa gwamnatin tarayya izinin tsare shi na tsawon kwanaki 15 a hannun hukumar leken asiri ta tsaro.
Daga bisani, alkalin ya umurci gwamnatin tarayya da ta gurfanar da shugaban na Miyetti Allah, ko kuma ta sake shi ya ci gaba da harkokinsa.