Rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 56 mai suna Oladimeji David a gaban wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti bisa zargin satar wasu bunsuru guda biyu.
Dan sanda mai shigar da kara, Johnson Okunade, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Maris da misalin karfe 4 na yamma a Ado-Ekiti.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Azama Wajen Dakile Hadurran Dake Tunkarar Tattalin Arzikin Duniya
- Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara
Okunade ya kuma yi zargin cewa wanda ake tuhuma ya saci bunsurun guda biyu na wani mai suna Alhaji Nurudeen Ambali da Olubodun Iyabo wanda kudinsu ya kai N80,000.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 320(1) (a) na dokokin laifuka na Jihar Ekiti 2021.
Lauyan mai gabatar da kara ya roki kotun da ta dage shari’ar don ba shi damar yin nazarin karar tare da gabatar da shaidunsa.
Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Lauya wanda ake kara, Misis Adunni Olanipekun, ta bukaci kotun da ta bayar da belin wanda take karewa.
Ta kuma tabbatar wa da kotun cewa wanda ta ke karewa ba zai tsallake beli ba.
Alkalin kotun, Mista A.O Adeosun, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N50,000 tare da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.
Ya dage sauraren karar har sai ranar 6 ga watan Afrilu don ci gaba da shari’ar.