• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Jinjina Wa Tawagar NPA Kan Samun Nasarar Sayar Da Danyen Mai Da Takardar Naira

by Abubakar Abba and Sulaiman
10 months ago
Gaza

Shugaban Karamin Kwamitin Fasaha na wanzar da tsarin Gwamnatin Tarayya na dayen mai da ake sayarwa na cikin gida da kayan da ake sarrafawa a kan takardar Naira Zacch Adedeji, ya jinjiawa tawagar shirin sayen kaya wato (OSS) wadda Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ke jagorantar tabbatar an gudanar da ayyukan a cikin nasara.

Adedeji wanda kuma shi ne, Shugaban Hukumar tara Haraji ta kasa ya ya yi wannan yabon ne, a lokacin da ya kai ziyarar aiki a shalkawatar Hukumar NPA a ranar Alhamis da ta gabata.

  • Zargin China Da Bautar Da Leburori a Gonar Tumatir a Xinjiang: Mene Ne Gaskiyar Lamarin?
  • Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda A Zamfara

Kazalika, Adedeji, ya godewa, tawagar ta Hukumar NPA, kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen wanzar da umarnin na fadara shugaban kasa na ayyukan sayar da danyen man a cikin gida Nijeriya da kuma sauran kayan da ake sararafwa kan takardar Naira

Adedeji ya kara da cewa,“Mun lura da namijin kokarin da tawagar ke kan yi wajen samun nasarar gudanar da ayyukan, wanda hakan ya kuma nuna irin kishin kasar da tawagar take da shi, na son cimma nasara”.

Ya ci gaba da cewa,“ A saboda haka, muna karawa tawagar kwarin guiwar da su kara zagewa da kuma mayar da hankali domin a samu cimma nasarar gudanar da shirin.”

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

Adedeji ya ce,“ Muna mika godiyar mu ga sauran hukumomi da suke a cikin wannan aikin, saboda irin dimbin goyon baya da hadin kai da suka bayarwa”.

Da yake mayar da na sa bayanin, Babban Manajin Darakta na Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, “ Wannan yabon da Kwamitin ya yiwa tawagar, zai karawa tawagar kwarin guiwa ne, wajen kara mayar da hankali kan shirin”.

Dakta Dantsoho ya kuma yi amfani da damar wajen yabawa ministan Tattalin Arziki na Albarkatun Ruwa Hon. Adegboyega Oyetola a kan samar da sahihin shuganaci na gari, wanda hakan ya taimaka, wajen samun cin nasarar shirin.

“Muna godewa namjin kokarin Shugaban Karamin Kwamitin Zacch Adedeji, musamman kan goyon bayan da yake bayarwa har ta kai ga, shirin ya samu cimma wannan nasarar”.

Kazalika, Dakta Dantsoho, ya bayya cewa, bisa samar da wannan shirin, na sayar da danyen man kan takardar Naira da kuma kayan da ake sarrafawa a cikin Nijeriya, hakan ya nuna yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taimaka wajen ragewa Nijeriya yin asarar biliyoyin Naira.

Dakta Dantsoho ya kara da cewa, hakan ya kuma bayar da wata dama na kula da fannin makamashi na kasar, kara zurafafa cinikayya, samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya, damar rage karancin albarkatun man fetur da kuma kawo karashen jerin Gwanonin layukan ababen hawa a gidajen sayar da man fetur na kasar, musamman a wannan lokutan na bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Wannan shirin dai na zuwa ne, daidai lokacin da matatar man fetur ta Dangote, ta rage farashin man da take samarwa samfarin PMS zuwa Naira 899.50 na kowacce lita daya,

Sauran tawagar da ke a cikin Kwamtin sun hada da Hukumomin NIMASA, NMDPRA, NUPRC, NEPZA, FIRS, NNPC, DAPMAN, IPMAN, PHS, MEMAN, NDLEA, Matatar Dangote, Kwantirola na Kwastam da kuma Hafsan Rundunar Sojin Sama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
Tattalin Arziki

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Next Post
Manyan Bankunan Kasa Na Sin Da Nijeriya Sun Sabunta Yarjejeniyar Musayar Kudi

Manyan Bankunan Kasa Na Sin Da Nijeriya Sun Sabunta Yarjejeniyar Musayar Kudi

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.