Aƙalla mutane uku, ciki har da ƙaramin yaro mai shekaru uku ne sun mutu sakamakon wani hari da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai wa al’ummar Omulonye da ke Ugboju Icho, a ƙaramar hukumar Otukpo ta Jihar Benue.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga yankin ne da yammacin ranar Laraba, inda suka jikkata wasu mazauna yankin da dama.
A halin yanzu, waɗanda suka jikkata suna karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a garin Otukpo.
Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce waɗanda ake zargin sun daɗe suna addabar yankin a baya-bayan nan.
Ya ce: “Waɗanda suka daɗe suna addabar yankin ne suka kashe mutane uku. Ƙaramin yaro ɗan shekaru uku na cikin waɗanda aka kashe.
“An kuma jikkata wasu waɗanda a yanzu suke karɓar magani a Otukpo.”
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benue, DSP Peter Orchia Aondongu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe mutane uku a yankin Ugboju da ke ƙaramar hukumar Otukpo.














