Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen Jihar Bauchi, ta gargaɗi ’yan jarida da su guji yaɗa rahotannin da ba su tantance sahihancinsu ba, dangane da zargin cewa an cire wani limami a Jihar Bauchi daga matsayinsa saboda ya yi kamfen wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.
An dai ruwaito cewa wani mutum mai suna Dahiru Abubakar da aka fi sani da Danmalam ya yi zargin cewa an cire shi daga limanci a wani masallaci da ke unguwar Madina Quarters a Bauchi, saboda ya tallata Tinubu.
A cikin wata sanarwa a Juma’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Comrade Isah Garba Gadau, da sakataren ta, Isiyaka Ismail Wunti, NUJ ta bayyana damuwarta kan yadda ake yaɗa zargin tare da tabbatar da inganci da sahihancin zargin ba.
NUJ ta ce binciken farko-farko da ta gudanar bai gano wata hujja da ke nuna cewa mutumin da ake magana a kansa ya taɓa samun naɗin limanci ko ya yi limanci a wani masallaci a cikin birnin Bauchi ko wani wuri a jihar ba.
A cewar ƙungiyar, binciken da ta gudanar ya kuma nuna cewa mutumin ya fi mayar da hankali ne kan neman suna ta harƙoƙin siyasa, lamarin da ya haifar da tambayoyi game da sahihancin iƙirarin da ya yi.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ya kamata ’yan jarida su tuntuɓi shugabannin masallacin ko kwamitin gudanarwarsa domin gano gaskiyar lamarin kafin wallafa rahotannin.
NUJ ta bayyana lamarin a matsayin tunatarwa kan haɗarin dogaro da iƙirarin mutum guda kawai ba tare da neman tabbaci daga wasu majiyoyi masu zaman kansu ko jin ta bakin waɗanda abin ya shafa ba.
Ƙungiyar ta jaddada cewa batutuwan da suka shafi addini da siyasa na buƙatar ta-ka-tsantsan na musamman, saboda yadda za su iya haifar da tashin hankali, tayar da rashin fahimta da kuma kawo barazana ga zaman lafiya.
Haka kuma, kungiyar ta nuna damuwarta kan abin da ta bayyana a matsayin rashin zurfafa bincike kan tarihin mutumin da kalaman da ya yi a bainar jama’a kafin a yaɗa iƙirarin nasa.
Ta buƙaci ‘yan jarida su yi amfani da hankali da tantance abun da ya dace su yaɗa wa jama’a, tare da bambance sahihan bayanai daga zarge-zarge, ra’ayoyin mutum da kuma iƙirarin siyasa.
Yayin da harkokin siyasa ke ƙara gabatowa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, NUJ ta gargaɗi ’yan jarida da kada su bari muradun siyasa, son zuciya ko neman ɗaukar hankalin jama’a su saɓa wa ƙa’idojin aikin jarida.
Ta sake jaddada cewa sahihanci, adalci, nuna gaskiya ba tare da son kai ba, inganci, su ne ginshiƙan aikin jarida nagari.
Saboda haka, NUJ ta buƙaci ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai a Jihar Bauchi su ƙarfafa hanyoyin tantance sahihancin bayanai, tabbatar da bayanai ta hanyar majiyoyi masu inganci, neman jin ta bakin waɗanda abin ya shafa tare da bayar da cikakken bayani game da al’amura kafin wallafa rahotanni masu muhimmanci, musamman waɗanda suka shafi addini, siyasa da tsaro.
Haka kuma, ta yi gargaɗin cewa ba za ta ɗauki wasa da ƙa’idojin aikin jarida da aka amince da su da wasa ba, inda ta tabbatar wa jama’a cewa ƙungiyar za ta ci gaba da inganta ƙwarewa da kuma kare mutuncin aikin jarida.
Sanarwar ta sake tabbatar da aniyarta na inganta aikin jarida bisa gaskiya da riƙon amana, tare da kira ga dukkan masu aikin jarida da su ba gaskiya, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma muradun jama’a fifiko yayin gudanar da ayyukansu.













