Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa aƙalla mutum 245 ne suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ya afku a sassan Nijeriya a cikin wannan shekara ta 2026. Bayanan da aka samu daga shafin tattara alkaluman hukumar sun nuna cewa mutum 673,350 ne ambaliyar ta shafa a ƙananan hukumomi 134 da ke faɗin jihohi 28 ya zuwa ranar 20 ga watan Oktoba, 2026.
Alkaluman sun ƙara fayyace cewa mutum 214,997 sun rasa muhallansu tare da zama ƴan gudun hijira a tsawon wannan lokaci. Da take jawabi a yayin taron masu ruwa da tsaki kan ayyukan agaji, Darakta-Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar wadda Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Hasashe, Dokta Godwin Topikor, ya wakilta ta bayyana cewa yawan asarar da aka yi ya nuna muhimmancin sake duba matakan agaji da ake ɗauka, da gano duk wani giɓin da ke akwai, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin biyan buƙatun al’ummomin da lamarin ya shafa.
Hajiya Zubaida ta jaddada buƙatar sanya ido sosai kan lafiyar al’umma da kuma sanar da ingantattun bayanai a kan lokaci, musamman a sansanonin ƴan gudun hijira inda rashin ingantaccen tsarin tsafta da ƙarancin kayan more rayuwa ka iya haddasa ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa. Ta kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su haɗa hannu wajen amfani da hasashen yanayi da gargaɗin farko don ɗaukar matakan kariya kafin iftila’i ya auku, domin kare rayuka, abin dogaro da kai, da kuma manyan ababen more rayuwa.
A cewar shugabar ta NEMA, sha’anin kula da ibtila’i yana buƙatar shiri na musamman da kuma haɗin kan ɓangarori daban-daban, tare da ba da fifiko ga kare marasa ƙarfi da suka haɗa da mata, da ƙananan yara, da tsofaffi, da masu buƙata ta musamman. Ta bayyana cewa an kafa Babban Dandalin Haɗin Gwiwar Agajin Gaggawa na Ƙasa (NECF) ne domin sake duba matakan da ake ɗauka a halin yanzu da kuma shirya tsare-tsaren tunkarar canjin yanayi na El Niño da ake sa ran zai iya aukuwa a tsakanin shekarar 2026 zuwa 2027.














