Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar wa iyayen ɗaliban da aka sace a makarantar St. Mary’s Catholic School a Papiri, Jihar Neja, cewa za a ceto yaran nan ba da daɗewa ba.
Ribadu ya isar da saƙon Shugaba Bola Tinubu yayin ziyararsa ga Bishop ɗin Katolika na Kontagora da iyayen yaran.
- Gwamna Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
- Za Mu Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro – Sarkin Fulanin Mubi
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto ɗaliban, kuma an tura ƙarin jami’an tsaro yankin.
Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya shiga damuwa sosai wanda hakan ya sa ya soke wasu ayyukan gwamnati saboda wannan lamari.
Ribadu ya buƙaci ’yan Nijeriya su kasance a haɗe, su kuma guji barin ’yan ta’adda suna raba su.
Ya ce ƙasashe kamar Amurka, Faransa da Birtaniya suna bai wa Nijeriya goyon baya, sannan ya yi alƙawarin ƙara tsaro a makarantar da unguwanninta.
Harin ya faru ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai farmaki makarantar cikin dare, inda suka yi garkuwa da mutane 315; ɗalibai 303 da malamai 12.
Ɗalibai 50 sun tsere a rana ta farko, amma mutane 265 har yanzu suna hannunsu.














