Muhammad Awwal Umar" />

An Nemi Kafafen Yada Labarai Su kara kaimin Wayar Da Kan Jama’a Muhimmancin Tazarar Haihuwa

An bayyana cewar kafofin yada labarai na da muhimmanci wajen yawar da jama’a, Kodinetan kungiyar The Challenge Initiative a Neja, Hajiya Zainab Baba ce ta bayyana hakan a lokacin zantawar ta da manema labarai juma’ar makon nan da ya gabata a Minna.
Hajiya Zainab, tace shirin wayar da kan jama’a muhimmancin tazarar haihuwa bai sabawa ka’idodin kiwon lafiya ba, domin shiri ne da zai taimaka wajen samun iyali mai inganci tare da hadin guiwar ma’aikatar kiwon lafiya ta jiha.
Tace tsarin kashi biyu ne, akwai tsari na gargajiya wanda addinin musulunci yazo da shi, sannan akwai tsari na zamani yazo da shi wanda kuma yana tafiya bisa shawarwarin masana kiwon lafiya.
Tace ba burin gwamnati takaita yawan jama’a ba, babban burin gwamnati shi ne samar da iyali mai inganci da cikakkiyar kiwon lafiya, tare da saukakawa iyaye wajen kula da tarbiya da ilmantar da yara masu tasowa.
Tace kungiyar The Challenge Initiative tana kokarin taimakawa gwamnati da ma’aikatar kiwon lafiya dubarun wayar da kan jama’a muhimmancin shirin, ta yadda har wadanda ke cikin karkaru zasu iya anfana da shirin ta hanyar samun sakon a kafafen yada labarai, wanda yasa tafiyar ba yadda za ta iya samun nasara sai da taimakon kafafen yada labarai da suka kunshi radio, talabijin da gidajen jaridu.
A na ta bangaren kuwa, Madam Glory Omomate, na Demand Generation, jami’ar da ke bada gudunmawa a kungiyar. Tace lallai kafafen radio da talabijin suna da muhimmanci musamman a shirin kai tsaye da suke gabatarwa, domin ya kan taimaka wajen baiwa mai sauraro damar kira kan abinda bai fahimta ba game da shirin, hakan yakan baiwa mai sauraro damar sanin abinda ya shige mai duhu.
A cewar wayar da kan jama’a bai tsaya kan gwamnati kawai ba, akwai bukatar kowa ya taka rawar gani wajen samun zamani mai inganci da zai taimaka wajen rage matsalolin da ake fuskanta saboda durkushewar tattalin arzikin kasa da ya shafi rayuwar jama’ar kasa.
Madam Glory tace aikin bai tsaya kan ‘yan jarida da ma’aikatan kiwon lafiya kawai ba, iyaye na da rawar takawa wajen ilmantar da ‘yayansu illar mu’amala tsakanin namiji da mace ba ta hanyar aure ba, wanda hakan zai taimaka gaya wajen rage yaduwar saduwa ba bisa hanyar da ta dace ba, in ma hakan ya faru bai kamata iyaye su yi fushi ba akwai hanyoyin da ya kamata su bi wajen ceton lafiyar ‘yayan su.
Shirin tazarar haihuwar dai da gwamnatin Neja ta kuduri aniyar aiwatarwa yana samun goyon bayan gwamnati na samar da duk abubuwan da suka da ce ga cibiyoyin da ke kula da shirin a dukkanin yankunan kananan hukumomi da ke jihar.
Yayin da kungiyar The Challenge Initiatibe ( TCI) ta ke cigaba da wayar da kan jama’a muhimmancin shirin tare da hadin guiwar manema labarai, inda take ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya dan sanin irin karbuwa da matsalolin da shirin ke fuskanta.

Exit mobile version