Yau Asabar aka rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) na 20 a birnin Beijing.
A yayin bikin rufe taron, wakilai 2338 mahalarta taron sun zabi kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, da kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin kolin.
Kana an zartas da kuduri game da rahoton kwamitin kolin jam’iyyar JKS karo na 19, da kuduri game da rahoton ayyukan kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin kolin karo na 19, da kuma kuduri kan gyararren kundin ka’idojin jam’iyyar.
Taron ya amince da shigar da sabbin nasarorin nazari kan tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a cikin kundin ka’idojin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Kuma bisa ga manyan ayyukan da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta sanya gaba a babban taron wakilan JKS karo na 20, an daidaita tare da kyautata bayani kan burin da ake fatan cimmawa a kundin ka’idojin jam’iyyar.
An kuma tabbatar da babban burin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, wato za mu cimma nasarar zamanantar da kasar Sin mai bin tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da gina kasar Sin ta yadda za ta zama kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu na zamani nan zuwa tsakiyar wannan karni, wato yayin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama’ar Sin.
Xi Jinping ya shugabanci bikin rufe babban taro, tare kuma da gabatar da jawabi. Inda ya jaddada cewa, jam’iyyar kwaminisanci ta kasar Sin ta shafe shekaru dari na gwagwarmaya, kuma ta bullo da wata sabuwar hanya domin daukar jarrabawar. Jam’iyyar tana da cikakken kwarin gwiwa da karfin samar da sabbin mu’ujizai da za su burge duniya a sabon zamani.
Ya kuma yi kira ga daukacin jam’iyyar da ta jagoranci al’ummomin dukkan kabilun kasar da su hada kai don gina kasa mai bin tsarin gurguzu na zamani bisa a dukkan fannoni, da kuma sa kaimi ga farfadowar al’ummar kasar Sin a dukkan fannoni. (Mai fassara: Bilkisu Xin)