Rabiu Ali Indabawa" />

An Sake Kai Hari Kan Masu kula Da Cutar Ebola A Congo

An yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan tawayen a lokacin harin, wanda aka kai a wani asibiti da ake kira Katwa. Wasu ‘yan tawaye dauke da muggan makamai, sun far ma wata cibiyar da ake kula da masu fama da cutar Ebola a kusa da birnin Butembo, da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Harin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani hari na daban, da ya yi sanadin mutuwar wani likitin Kasar Kamaru da ke taimakawa masu fama da cutar, inji ‘yan sandan Kasar.
An yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan tawayen a lokacin harin, wanda aka kai a wani asibiti da ake kira Katwa, inda anan ne ma’aikatan lafiya ke kokarin dakile yaduwar cutar, wacce ta barke a gabashin Kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Mataimakin Magajin gari, Patrick Kambale, ya ce maharan sun yi kokarin kona cibiyar ne a daren jiya.

Exit mobile version