Majalisar zartarwar Jihar Kano ta amince da mayar da Jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, tare da ci gaba da bayar da takardun digiri.
An yanke wannan hukuncin ne a zaman majalisar na 18, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan irin sauyin da mayar da ita a jami’a zai haifar da suka haɗa da yiwuwar rasa kwararrun malaman jami’a da kuma rikicin albashi.
- Gwamnan Kano Ya Rushe Kantomomin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44
- Gwamnati Za Ta Gina Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa Sabbin Gidaje A Kano
Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa jihar ta zaɓi tsarin “Dual Mode”, wanda zai bai wa cibiyar damar ci gaba da zama kwaleji tare da bayar da shirye-shiryen digiri. Wannan mataki ya samo asali ne don samar da tsari mai ɗorewa ga ci gaban makarantar.
An tabbatar wa ɗalibai cewa wannan sauyinn ba zai shafi karatunsu ba, kuma kwalejin za ta ci gaba da shirye-shiryen ta na farko da sabbin digiri. Bugu da ƙari, za a adana takardun shaidar jami’ar don amfani a nan gaba, tare da samar da damar sauya alkibla idan buƙatar hakan ta taso.
Hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa NCC ce dai ta amincewa Kwalejin komawa jami’a a watan Fabrairun shekarar 2023 lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.