Rikici ya sake mamaye wasu sassa na karamar hukumar Jos ta arewa, a bisa wasu rahotannin da ba su da tabbas na cewa wasu ‘yan ta’adda da ke dauke da makamai suna tsare da wasu daliban Jami’ar Jos, ta Jihar Filato.
Rikicin wanda ya sake barkewa a ranar Lahadi da rana, bayan kashe mutane sama da 20 a kan hanyar Rukuba, Jos, an yi zargin cewa, masu dauke da makaman sun tsare manyan tituna da ke kewayen kauyan da kuma gidan kwanan dalibai na Naraguta, da ke Jos ta arewa, suna ta harbi da kashe mazauna wajen da kuma sauran masu bi ta hanyar.
Binciken wakilinmu ya bayyana cewa, kawo yanzun, an yi zargin an harbi dalibai uku a kauyan Rusau, da ke kusa da Jami’ar ta Jos, sa’ilin kuma da aka shelanta bacewar wani dalibin mai karantar hada magunguna dan aji biyu.
Ana ta kuma samun kiraye-kirayen neman dauki daga sassan da abin ya shafa har kawo lokacin hada wannan rahoton.
Ana jin gazawar da jami’an tsaro suka yi na kawo dauki domin kwantar da rikicin ya faru ne a sakamakon yanda aka tura dandazon jami’an tsaron wuraren da ake gudanar da zabukan fitar da gwani na Jam’iyyun APC da na PDP, domin su baiwa ‘yan siyasa kariya.
Gwamnatin Jihar ba ta ce komai ba tukunna a kan lamarin, sai dai, Gwamnan Jihar ta Filato, ya tabbatar wa da dukkanin wakilan da suka halarci wurin zaben fitar da gwanin na Jam’iyyar APC cewa za a hada su da rakiyar Jami’an tsaro domin su koma wuraren da suka fito bayan an kare zaben.
A yanzun haka dai, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar ta Filato, Undie Udie, ya umurci mazauna unguwannin, Dutse Ukwu, Marabar Tina, Rikkos, Angwan Rukuba, Farin Gada, da mazauna dakunan kwana na Jami’ar ta Jos, da su zauna a cikin wuraren da suke.
Cikin tattaunawar da aka yi da Kwamishinan na ‘yan sandan Jihar jiya da dare a Jos, Kwamishinan ya tabbatar da cewa, gamayyar jami’an tsaro na Soji da ‘yan sanda suna gudanar da zagayen aiki a wadannan sassan domin su kwantar da rikicin, duk kuma wanda aka samu a waje a wadannan sassan za a kama shi a kuma hukunta shi.
Ya gargadi al’umma da su kiyaye da wadannan Unguwannin da aka ambata.