An samu rarrabuwar kawuna a jam’iyyar ADC kan sahihancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark a yayin da wani tsagi na jam’iyyar ya nuna bai amince da shugabancin rikon kwaya ba a halin yanzu.
Wannan ya faru ne a lokacin da wani bangare na jam’iyyar da tsohon dan takarar gwamnan Jihar Gombe, Nafiu Bala yake jagoranta ya yi ikirarin cewa shugabancin rikon gwarya na Dabid Mark ba halastacce ba ne kuma ya saba wa kundin tsarin jam’iyyar.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga Bala kan al’amuran jama’a, Dakta Aminu Alhassan ya Sanya wa hannu, ya ce tsagin ADC ya jaddada cewa kawai mambobi na asali wanda su ne ya kamata a bai wa jagorancn jam’iyar.
Ya ce, “Dangane da takardar murabus na Cif Ralph Nwosu, mun lura cewa wasu mutane, musamman Dabid Mark da abokansa, su ne suka yi kokarin bayyana ikirarinsu na jagorancin jam’iyyar, wanda hakan ya sab awa ka’idoji da kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya shimfida.
“Da farko dai, yana da muhimmanci a fayyace cewa murabus din Ralph Nwosu ba ta haifar da yanayi mai kyau ba ga kowa da ke cikin ADC. Ma’ana, ta bude tattaunawa mai muhimmanci game da makomar jagorancinmu, tattaunawa da ya kamata a gudanar bisa tsarin da kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya kafa.
“Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba.
“A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike gurbin jagoranci bayan tafiyar Cif Nwosu ita ce, ta hanyar taron kwamitin zartarwa na kasa.”
Tsaagin jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa Alhaji Nafiu shi ne halastaccen shugabanta na kasa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da hadin kai.
Ya kuma bayyana kwarin giwa kan ikon hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na kiyaye ka’idojin kundin tsarin mulki da na dimokuradiyya a cikin harkokin jam’iyyar siyasa.
Ya kara da cewa, “Wannan taron zai zama dandalin tattaunawa kan hanyar ci gaba kuma za a biyo bayansa da tantancewa a matakai na gaba na taron jam’iyyar. Wannan ne inda za mu tabbatar da cewa jagorancin jam’iyyarmu an kayyade ta ne daga wadanda ke da gaske suna sha’awar ra’ayoyi da manufofin ADC.”
“Muna so mu jaddada cewa babu wani tanadi a cikin tsarin dokokin hukumar zabe da tsarin mulki ko dokokin jam’iyyar ADC da ke ba mutum damar karbar jagoranci ba tare da cika sharuddan zama mamba ba da tsarin dimokuradiyya ya tanada.
“Ayyukan da Dabid Mark da abokan huldarsa ke yi ba kawai saba wa tsarin mulkin jam’iyyarmu ba ne, yana kuma nuna rashin girmamawa ga ka’idojin dimokuradiyya da ADC ta tsayu a kai.
“Muna kira ga mambobinmu masu muhimmanci da jajircewa, ku da ku kasance cikin zaman lafiya da kuma mayar da hankali a wannan lokaci na neman samun sauye-sauye. Ci gaban da muka yi a matsayin jam’iya shaida ce ga aikin tukuru da jajircewar mambobinmu na asali.
“Dole ne mu kalubanci abubuwa marasa kyau na wadanda ke son kawo cikas ga hadin kanmu da ci gabanmu. ADC jam’iyya ce da aka gina bisa ginshikin gaskiya, hadin kai, da dabi’un dimokuradiyya, kuma dole ne mu yi aiki tare wajen kare wadannan ka’idoji.
“A daidai wannan lokaci, muna kuma son tabbatar da cewa muna da kwarin giwa kan hukumar zabe ta kasa wacce ba ta dogaro da gwamnati da shiga cikin wannan lamari. Muna yarda da sadaukarwarta wajen tabbatar da bin doka da tsari da tabbatar da cewa ana girmamawa kuma ana bin tsarin dimokuradiyya a cikin jam’iyyun siyasa. Jam’iyyar ADC ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki tare da INEC don inganta yanayin siyasa wanda zai kasance mai kyau tare da martaba tsarin dimokuradiyya.
“A karshe, muna goyon bayan Alhaji Nafiu a matsayin shugaban jam’iyyar ADC na gaskiya. Jagorancinsa zai zama mai mutunta ka’idojin jam’iyyarmu a wannan lokaci na canji, kuma muna da tabbacin cewa zai kula da hakkin asalin mambobinmu masu daraja. Muna kira ga dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar ADC na asali su goyi bayan Alhaji Nafiu da kuma aiki tare da shi don inganta jam’iyyarmu da al’umar da muke yi wa hidima.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp