Shugaban kungiyar Manoma Auduga (COPMAN) na Jihar Gombe, Alhaji Sadik Ado, ya yi kira ga manoma auduga a Nijeriya, da ka su sare wajen garin sun wadatarda kasar da ingantaccen auduga da za ta zama abin alfahari ba a Nijeriya kadai ba, harma da kasashen duniya baki daya.
Ya yin da yake tattaunawa da wakilan mu a Sakatarial din kungiyar da ke babban Titin Gombe zuwa Biu ranar Litinin, Alhaji Ado ya lura da cewa, cikin shekarun nan, musaman tsakanin Shekara 2019 zuwa 2021, noman auduga ta bunkasa nesa ba kusa ba, kuma gaba kadan, tasirin ta zata haura abin da aka girba a baya.
- Yadda Ya Kamata Hausawa Su Gudanar Da Bikin Aure – Masana
- Ku Nisanci Shiga Siyasa, GargaÉ—in INEC Ga Sabbin Kwamishinoninta
A cewar shi, “yau a samu kadadagar gonakin auduga a ko ina a kasar nan, musamman a nan Arewaci, tun da an samu Karin hektar filayen audugan daga hektar 194 zuwa kusan 2000 a yau, ya yin da matasan manoman audugar masu kananan zango wato (SHF), sun haura Miliyon uku”.
Ado wanda shi ne kuma mataimakin Shugaban Kungiyar ta COPMAN na kasar reshen Arewa Maso Gabacin Nijeriya, ya yi nuni da cewa, shirin nan na Babban Bankin Nijeriya na tallafawa kungiyoyi wato (Anchor-Borrower Programe – ABP), ya yi matukar tasiri ga manoman auduga, musamman daga shekarar 2017 – 2021 lokacin da aka samun karin sama da tan 120,000 fiye da shekarun 2011, 2015 da 2021, yana mai karawa da cewa, dadin dada, jimlar audugar da aka noma, ta anfanar da dubban manoma da masu sussuka da masakai.
Shugaban ya kara da cewa, tsarin auduga ta fara re tu locacin da Turawa suka budde B.C.G.A. a biranen Nijeriya daban – daban, wadan a yau bayan shekaru, an sake kara farfado da kara bunkasa noman auduga inda Nijeriya ce kasar da ta dara ko wase kasar a Afurka wajen noman auduga, duk da wasu kalubale kamar rikicin manoma da makiyayya da ambaliyar ruwa da makamantan su. “Amma Alhamdu Lillahi, muna ta ci gaba da no ma auduga kuma da yawa manoman mu sama da mutum 10,000, sun amfana da bita da horo iri – iri ta yadda za su noma ingantancen auduga ga kasar mu, har mu fitar kasashen waje”, inji shi.
Sai Alhaji Ado ya yi kira ga kungiyoyi da wadanda alhakin ya rataya a Kansu, da su tabbata sun rarrabawa manoman su duk muhimman kayayyakin noma auduga musamman taki a kan lokaci, kuma gana kara shawara ga manoma da suke kabir rance, suyi kokari su bia duk abin da ake bin su domin su samu damar samu wani rancen kuma, bays ga kuma baiwa wasu damar morar rancen suma