Rundunar haɗin gwuiwa ta MNJTF ta yi nasarar kai wani sumame da ya yi sanadin miƙa wuyar ƴan ta’addar ƙungiyar IS guda uku tare da kuɓutar da mutane 34 da suka yi garkuwa da su, da suka haɗa da mata da ƙananan yara daga yankin kudancin tafkin Chadi.
Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, babban jami’in yaɗa labarai na rundunar soji na MNJTF, ya bayyana cewa, a ranar 15 ga watan Yuni, 2024, aikin kakkaɓe ƴan ta’addan a ƙauyukan Mazuri, Itsari, Mudu, da Maleri ya kai ga tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe wani dan tada kayar baya.
- NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
- Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi
A ranar 17 ga Yuni, 2024, mayakan ISWAP uku daga sansanin Jabilaram da ke tafkin Chadi, waɗanda aka bayyana sunayensu da Babakura Abubakar, Abacha Kyari, da Mohammad Adam, sun miƙa wuya ga dakarun sa-kai. Yanzu haka dai ana ci gaba da yi wa mayakan tambayoyi domin samun ƙarin bayanan sirri kan ayyukan ta’addanci.
Wannan ci gaban wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na raunana karfin aiki da kwarin gwiwar duk ƴan ta’adda a yankin.
A ci gaba da inganta nasarar hare-haren da aka kai a ranar 9 ga Yuni, 2024, a Kollaram, sun lalata na’urori masu fashewa da suka haɗa da ƙunar bakin wake guda uku da ke shirin kai wani gagarumin hari.
Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali, Kwamandan Rundunar MNJTF, ya yaba da bajintat sojojin tare da jaddada aniyar rundunar na kawar da ta’addanci, tabbatar da tsaron fararen hula, da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi.