Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa, inda ya bayyana matsalolin lafiyar iyalinsa a matsayin babban dalilin da ya sa zai ɗauki hutu na ɗan lokaci. Sai dai, wasu majiyoyi na nuna cewa akwai wani dalilin ajiye aikin nasa saɓanin yadda aka bayyana.
Rahotanni sun nuna cewa ficewar Ngelale daga fadar shugaban ƙasar ta samo asali ne daga rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa a tsakanin tawagar watsa labaran shugaban ƙasar.
- Bola Tinubu Da Wasu Shugabannin Afirka Sun Iso Beijing Don Halartar Taron FOCAC
- Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Yar’adua
Ana zargin cewa akwai matsin lamba na a sauya shi da wanda ake ganin yana da kyakkyawar alaka da manema labarai da kuma mafi dacewa da ra’ayin shugaba Tinubu.
Bugu da ƙari, yadda ya ke gudanar da ayyuka daban-daban – daga matsayinsa na mai magana da yawun shugaban ƙasa zuwa mukaman wakilin shugaban ƙasa kan sauyin yanayi da kuma shugaban kwamitin kula da aikin Project Evergreen – ya shafi aikinsa na asali a harkokin watsa labarai.
Rikicin cikin gida da sauran ma’aikatan watsa labarai, tare da yadda tasirinsa ke ƙaruwa a ɓangaren sauyin yanayi, sun ƙara janyo wannan rashin jituwa.
Lamarin ya kai ga an umarce shi ya zaɓi tsakanin ci gaba da zama mai magana da yawun shugaban ƙasa ko kuma mayar da hankali kan aikin sa na sauyin yanayi. Da ya zaɓi ci gaba da mukaminsa na mai magana da yawun shugaban ƙasa, an zargi wasu daga cikin manyan na kusa da shugaban ƙasa da yin katsalandan, wanda hakan ya janyo ajiye dukkan mukaman nasa.
Wasu majiyoyi sun nuna cewa shugaba Tinubu na iya naɗa tsohon Shugaban Ma’aikatansa, Sunday Dare, a matsayin wanda zai maye gurbin Ngelale, duk da cewa ba a tabbatar da wannan ba.
Ngelale bai ce komai ba a fili game da wannan batu, kuma duk wani ƙoƙari na samun karin bayani daga gare shi ya ci tura kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.