An yanke wa wata uwa mazauniyar Jihar Idaho ta Amurka da ke cikin wata kungiyar asiri ta masu hasashen aukuwar bala’i, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan an same ta da laifin kashe ‘ya’yanta masu tasowa biyu tare da hada baki wajen kashe kishiyarta.
An samu Lori Ballow Daybell, mai shekara 50, da aikata babban laifin kisan kai da tuhume-tuhume hada baki don aikata laifi a watan Mayu.
- Hanyoyin Da Suka Kamata ECOWAS Ta Bi Wajen Warware Rikicin Nijar
- Warware Jita-jita Masu Alaka Da Kwararon Roba (Condom)
Lori Ballow ta kashe danta Joshua wanda ake yi wa lakabi da “JJ” Ballow, dan shekara bakwai da ‘yarta Tylee Ryan ‘yar shekara 16.
An gano gawawwakinsu ne binne a cikin gidan mijinta Chad Daybell a shekara ta 2020.
A ranar Litinin, Mai shari’a Steben Boyce ya yanke wa Lori Ballow hukuncin daurin rai da rai har sau uku, ba tare da yiwuwar samun sakin je-ka-mu-ga-hankalinka ba.
“Kisan kai mafi munin da ba za a iya kwatantawa ba shi ne wanda uwa za ta halaka ‘ya’yan cikinta, kuma shi ne hakikanin abin da kika aikata,” Mai shari’a Boyce ya ce,
Kotu ta saurari bayanan shaidu masu ratsa zuciya daga dangin mijinta a lokacin yanke hukuncin.
“Tylee da JJ sun kawo dumbin haske a wannan duniya,” Colby Ryan, wani babban ‘ya’yansu ya fada a cikin wani jawabi da masu shigar da kara suka karanta.
“Ina son a rika tunawa da su kamar yadda Allah ya halicce su amma ba a matsayin wani abin kallo ko abin buga labarinsu a jaridun duniya ba.”
Mijinta, Chad Daybell shi man an tuhume kan mutuwar ‘ya’yan da kuma mutuwar tsohuwar matarsa, Tammy Daybell, makonni kafin ya auri Lori Ballow. An tsara gudanar da shari’arsa a cikin shekara mai zuwa.
Chad Daybell marubuci ne da ya wallafa litattafan tashin duniya bisa koyarwar addinin Mormon.