An zargi wata ‘yar siyasa, bangaren jam’iyyar hamayya a kasar Malawi da yunkurin kashe shugaban kasar, Lazarus Chakwera.
Patricia Kaliati, wadda ita ce sakatare-janar a jam’iyyar UTM, ta shiga hannu ne a makon jiya bisa zarginta da “hada baki da wasu domin aikata babban laifi.”
Da ta bayyana a kotu a jiya Litinin, ‘yar siyasar mai shekara 57 ba ta ce komai ba, amma lauyoyinta sun musunta zargin da ake mata, kamar yadda kafofin sadarwa a kasar suka ruwaito.
Wasu dai suna zargin cewa kama ta da aka yi ba ya rasa nasaba da bambamcin siyasa.
Alkalin kotun ya amince ya bayar da belin Kaliati, duk da cewa mai gabatar da kara ya bukaci a rike ta zuwa mako mai zuwa.
A bangaren ‘yansanda kuwa, sun ce suna aiki ne da doka, kuma za su kiyaye dukkan hakkinta.