Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Mai Shari’ a Rabiu Danlami A Kano

Rasuwar

Daga Haruna Akarada,

Ana cigaba da gudanar da ta’aziyya ta jimamin rasuwar Mai Shari’a Rabiu Danlami Mohammad a Jihar Kano.

A makon da ya gaba ta ne dai Allah ya yi wa Mai Shari’a Rabiu Danlami rasuwa; rasuwar da ta girgiza jama’a a Jihar Kano.

Justice Rabi’u Danlami kafin rasuwarsa alkali ne a kotun daukaka kara ne (Court of Appeal). Ya yi Kwamishinan shari’a a Jihar Kano, sannan ya yi shugaban daidai ta iyaka na Nijeriya.

Wannan bawan Allah mutum ne na jama’a wannan ce ta sa mai girma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci ta’aziyyarsa a unguwar Sharada Karamar Hukumar birni, ya baiyana mai Shari’ a mutum ne mai iya zama da muta ne ya yi fatan Allah ya jikansa.

Shi ma Ministan Gona, Alhaji Sabo Nanono, ya sami halaratar ta’aziyya. Sauran sun hada da Tsohon Sakataren gwamnati Yayale Ahamad da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Gali Umar Na-Abba da sauransu.

Exit mobile version