Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba komai ba ce illa rabin jikin PDP da ya rube, saboda kashi 80 na ‘ya`yan APC duk tsofaffin ‘yan PDP ne.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Arise a kwanan nan game da fagen siyasar Nijeriya.
- Nijeriya Ta Musanta Iƙirarin Binance Na Zargin Cin Hancin Dala Miliyan 150
- Majalisar Dattawa Za Ta Kafa Dokar Kare Hakkin ‘Yan Aikatau A Nijeriya
Da yake mayar da martini kan maganar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi a makon da ya gabata na cewa babu gurbi a kujerar shugabancin Nijeriya a 2027, Lamido ya ce magana ce kawai ta ‘yan siyasa, domin tsarin mulki ya bayar da damar gudanar da zabe duk bayan shekaru 4.
Lokacin da aka tambaye shi game da ziyarar gwamnonin arewa a Amurka kan batun tsaro, ya ce yana matukar girmama ofishinsu na gwamnoni, amma ko kadan bai dace su tafi har Amurka ba saboda tattauna matsalolin tsaron Nijeriya.
A cewarsa, jam’iyyar APC ta zo kan karagar mulki ne ba tare da manufofi ba, amma lokacin da PDP ke kan karagar mulki akwai dimbin manufofin da suka tsara gudanarwa domin ci gaban Nijeriya. Don haka ba za a taba hada hada gwamnatin PDP da ta APC ba, domin akwai bambanci sosai.
Kazalika, Sule Lamido ya ce sun ga yadda majan APC ta kasance ga ‘yan Nijeriya, wanda shi ya sa bai amince da manufar yin majar jam’iyyu saboda karbar mulki ba kawai, “na fi kaunar majan da za ta zo da kaykkyawar manufar yi wa ‘yan Nijeriya aiki. A lokacin da APC ta kulla maja a 2014 da sauran jam’iyyu ba su da wata mafufa illa iyaka su amshi shugabanci, sannan lokacin da suka hau karagar mulki kuma, majan ba ta amfanar da ‘yan Nijeriya ba. Don haka dole ne idan har za a yi maja ya kasance an bayyana manufofin da ake son cimmawa ba don amsar mulki ba kadai.”
Tsohon gwamnan, ya jaddada cewa lallai jam’iyyar PDP za ta dawo cikin hayyacinta duk da irin rikicin shugabanci da ta tsinci kanta a ciki. Yana mai cewar jam’iyyar ta shiga rikici mai yawan gaske ne sakamakon yadda wasu ‘ya`yanta ke yi wa APC aiki don durkusar da ita.
Ya bayyana yadda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suke ficewa daga jam’iyyar da cewa hukuncin kotu ne ya haddasa lamarin, sannan kuma wasu na jin tsoron Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arzikin Kasa da Badakalar Kudi (EFCC), inda hakan ke sa su komawa jam’iyyar APC domin su kubuta daga zunubansu, “kamar yadda tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomole ya taba fadar cewa, duk wanda ya shiga APC za a yafe masa zunubin da ya aikata ba.” In ji shi.
Dangane da sha’anin tsaro kuma, Sule Lamido ya ce akwai babbar matsala wajen magance tsaro a kasar nan, domin an samu gazawar shugabanci wanda kuma babban illa ce ga al’umma masu tasowa. Yana mai yin kiran a kara matsa kaimi don magance tsaro a kasar nan, da samun shugabanci nagari da zai hada kan matasa masu tasowa.