Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Za Ta Taya Wilfred Zaha Fam Miliyan 40

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shirya fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace domin siyan dan wasan kungiyar, Wilfred Zaha, wand Arsenal din take ganin fam miliyan 40 kawai zata iya biya domin siyansa.

Kungiyar Arsenal dai tana daya daga cikin kungiyoyin Manchester United da Tottenham da Bayern Munchen da Borussia Dortmund da suke son siyan dan wasan na gaba dan asalin kasar Ibory Coast.

Tuni dan wasan ya bayyanawa kungiyar tasa cewa yanason barin kungiyar domin buga kofin nahiyar turai sai dai kungiyar ta sa ta ce bazata siyar da dan wasan ba kasa da fam miliyan 80 farashin da ake ganin Arsenal bazata iya biya ba.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa kungiyarsa zata iya biyan rabin kudin ne kawai matakin da ake ganin kungiyar ta Crystal Palace zatayi fatali da tayin da Arsenal zatayi anan gaba.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wadda zata buga wasan karshe na gasar kofin Europa zata hadawa kungiyar Palace da ‘yan wasanta da suka hada da Collum Chambers da Carl Jenkinson sai kuma Reis Nelsen domin dai a siyar mata da dan wasan.

Shugabannin Arsenal dai sun ware kudi fam miliyan 40 domin bawa kociyan kungiyar a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa kudin da ake ganin sunyi kadan idan har kungiyar tanason tayi kokari a kakar wasa mai zuwa.

Exit mobile version