ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da bayyana dalilan sa da suka shafi saɓani da karkacewar jam’iyyar daga ainihin manufofinta na kafuwa.

A wata wasiƙar da aka sanya wa kwanan wata 14 ga Yuli, 2025, wacce ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Jada 1, a ƙaramar hukumar Jada ta jihar Adamawa, Atiku ya rubuta cewa: “Ina rubuto wannan wasiƙar ne don sanar da ku hukuncin ficewata daga jam’iyyar PDP daga wannan rana.”

  • Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku
  • Zan Yaƙi Duk Wanda Ya Yi Sata Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Atiku

Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 tare da kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasa sau biyu a ƙarƙashin PDP, ya bayyana cewa wannan mataki yana da matuƙar nauyi da raɗaɗi a zuciyarsa. “A matsayin ɗaya daga cikin waɗanda  suka kafa wannan jam’iyya mai daraja, ficewa daga cikinta abu ne mai matuƙar raɗaɗi gare ni.”

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa akwai saɓani da aka gaza sulhu tsakaninsa da jam’iyyar, inda ya bayyana cewa PDP ta gushe daga ainihin hanyarta. “Na yanke shawarar ficewa ne saboda yadda jam’iyyar ke tafiya yanzu ya sha bamban da manufofin da muka tsaya a kai tun farko.”

Atiku ya kammala wasikar da godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da goyon bayan da ya samu tsawon shekarun da ya kwashe a cikinta. “Ina fatan jam’iyya da shugabanninta za su yi nasara a gaba. Na gode bisa damar da aka ba ni.”

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

An tabbatar da karɓar wasiƙar ficewar a ofishin gundumar PDP ranar 14 ga Yuli, 2025, tare da sanya hannu da hatimin karɓa daga wani wakili mai suna Hamman Jada Abubakar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Next Post
An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano

An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.