Muhammad Awwal Umar" />

Atiku Nada ‘Yancin Zuwa Kotu Neman Hakkinsa –Wanna

An bayyana cewar rashin amincewar abokin hamayya idan an kada shi zabe ba bakon abu ba ne, domin ya faru a baya wanda wasu in sun fara bin kadin abin a kotu har sai sun kure, dan haka yau idan Abubakar Atiku ya ce, bai yarda da sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a makon jiya ba, wannan ba zai dada ‘yan Najeriya da kasa ba. Wani tsohon dan siyasa kuma basarake jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Muhammadu Awaisu Wanna ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, lahadin makon jiya a Minna.
Alhaji Awaisu ya cigaba da cewar idan Atiku ya tafi kotu yana da daman hakan kasancewarsa dan Najeriya, domin dokokin kasar nan sun amincewa duk wanda ya shiga zabe kuma bai gamsu ba yana da damar zuwa kotu dan tantance abinda ya shige mai duhu. Amma a wannan bagiren bai kamata Atiku ya tsaya bata lokacinsa ba domin sakamakon zaben ya nuna inda talakan kasar nan ya huskanta.
Lokacin da tsohon shugaban Goodluck Jonathan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi tazarar kuri’a sama da miliyan biyu ne kuma ya amince da sha kasa ya mikawa Buharin mulki, balle yanzu da Buharin ya baiwa Atiku tazarar kuri’a sama da miliyan hudu, idan har wanda ba musulmi ba zai iya rungumar kaddara mai zai hana Atikun ya hakuri kila Allah Ya ba shi wani abin da yafi wanda yake nema a yanzu.
Shugaba Buhari ya bayyana manufofinsa na yaki da rashawa, gyaran tattalin arzikin kasa, tsaro da sauransu kan haka talakan Najeriya ya ga sake ba shi damar dawowa karo na biyu dan tabbatar da wannan kuduri, :yan Najeriya ba su gamsu da manufar sayar da matatun man kasar nan da Atiku yace zai yi ba, to kila idan aka yi wannan ba su gamsu ba kila su ba shi damar gwada wannan a gaba amma dai yanzu Atiku yana neman suna ne ba wai shugabancin kasar da gaskiya ba.
Idan ana maganar shugaba Buhari ya tafi kotu a baya, ai ba irin wannan zaben ba ne domin kowa ya shaida a baya an arigizon kuri’u duk da ma cewar an yi lokacin da a Abuja kawai ake sanar sakamakon zaben da aka ga dama, shin da ya tafi kotun abin ya yi tasirin ne duk da yana da gaskiyarsa balle ma yanzu da sanin kowa da kuma amincewar ‘yan Najeriya bisa gamsuwa da wadannan zabukan, shi ko ba ka fita ba ne ka yadda jama’a suka fito da kwarin guiwarsu akan zaben, wannan ba majaujawa aka kada ba, zabe aka yi tsakanin karya da gaskiya saboda haka maganar magudi ko aringizon zabe a wannan lokacin da talaka yake neman ‘yancinsa ba gaskiya ba ne, domin mun gamsu da zaben kuma talaka yayi zabin da yake ra’ayi ne. Domin duniya ta shaida an yi zabe akan gaskiya, ai a shekarun baya kuri’ar talaka bada wani tasiri domin magudi ake yi, sai aje gidajen masu kudi a cika akwati da kuri’u a zo mazabu a tarwatsa mutane a maye gurbinsu da zalunci kuma wannan lokacin yazo karshe.
Saboda haka idan Atiku na da muradin zuwa kotu dan ganin yana da abin kashewa ga lauyoyi sai ya tafi amma dai talaka ya zabi abinda yake so kuma dole a bashi abinda ya zaba din nan, dan haka shugaba Buhari zai cigaba da shugabancin kasar nan har 2023, idan Atiku na sha’awar sake takara ne ko dan dacewa to ya hakura har Buhari ya kammala wa’adinsa da kuma cika alkawurran da yai wa mutanen kasa.
Shin maganar cewar Atiku ya gindaya ka’idojin da zasu hana shi zuwa kotu, muna yaki ne a kasar nan, ba zabe ne muka yi ba, kai koda yakin ma ake ba zama ake yi a dubi mai gaskiya a bashi gaskiyarsa ba, zabe ne fa aka yi kuma ‘yan kasa sun zabi abinda suke so, to ina maganar ka’ida kuma nan, Atikun yafi ‘yan Najeriya sama da miliyan dari biyu hakki ne a kasar, ban ga anfanin wadannan ka’idojin ba, dan Allah su bar Buhari ya fuskanci nauyin da ke kansa, wanda duk yake ganin yana da hakki ya tafi kotu kada’an, kasar nan muna bukatar tsayayyen shugaba ne da zai iya hubbasa wajen dakushe kaifin rashawa, tsaro tare da mai do da martaban tattalin arzikin mu da duniya ta sanya ido ta gani, dan haka jama’a mu tsaya mu taya maigirma shugaban kasa angon Najeriya addu’o’in samun nasara da sauke nauyin da ke kansa.

Exit mobile version