Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai wa dakataccen dan majalisar dattawa mai wakitar Bauchi ta tsayina, Sanata Abdul Ningi ziyara.
A lokacin wannan ziyarar a gidan Ningi, Atiku ya bukaci majalisa kar ta amince da zalunci, sannan ya jaddada muhimmancin majalisar dattawa wajen gudanar da harkokin gwamnati.
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
- APC Da PDP, Duk Kanwar Ja Ce -Kwankwaso
A ranar 12 ga Maris ta 2024, majalisar dattawa ta dakatar da Ningi har na tsawon watanni uku bisa zarginsa na karya dokokon majalisa lokacin da yake kokarin fallasa cushe a cikin kasafin kudi. Ya ce majalisa ta amince da kasafin kudin 2024 na naira tiriliyan 25, yayin da ita kuma gwamnatin tarayya ta bayyana naira tirili-yan 28.7. Ningi ya yi ikirarin cewa akwai ayyukan naira tiriliyan 3 da aka cusa a cikin kasafin kudin ba tare da bayani ba.
Lauyan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Umeh Kalu ya ce dakatarwar da aka yi wa Ningi mataki ne na majalisar ba na Akpabio ba.
Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya bayyana tarihin gudanar da harkokin gwamnati tare da kira ga majalisa kar ta amince da zalunci.
Ningi da Atiku sun yi kus-kus tare da jaddada muhimmancin rike mukamin siyasa wajen hidimta wa al’umma fiye da samun riban kashin kai a kowani mataki na siyasa.