Ruhin Doguwar Tafiya Ya Haskaka Dalilin Cimma Nasarar JKS Kamar Yadda Binciken CGTN Ya Shaida
A shekarar 1936, dan jarida Ba’amurke Edgar Snow, ya gabatarwa duniya JKS ta littafinsa mai taken Red Star Over China,...
A shekarar 1936, dan jarida Ba’amurke Edgar Snow, ya gabatarwa duniya JKS ta littafinsa mai taken Red Star Over China,...
Da safiyar yau Laraba, firaministan kasar Sin Li Qiang da takwaransa na kasar Rasha Mikhail Vladimirovich Mishustin, sun jagoranci taron ganawar firaministocin kasashen Sin da Rasha karo na 31 a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. A yayin taron, bangarorin biyu sun cimma raayi daya, cewa jagorancin da shugabannin kasashen biyu suka bayar, ya zama muhimmin tabbaci ga ci gaba mai dorewa na dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Haka kuma, ya kamata a bi raayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, domin inganta hadin gwiwa a fannoni da dama, kamar ciniki da zuba jari, da albarkatu da makamashi, da hada-hadar sufuri da sadarwa, da ayyukan sararin samaniya, da harkokin kudi, da kuma masana'antu da dai sauransu, baya ga samar da sabbin damammakin da za su haifar da ci gaba a fannoni na zamani, kamar fasahar AI, da fasahar kere-kere ta fannin halittu, da kuma tattalin arzikin zamani na dijital da dai sauransu. Haka kuma, ya kamata kasashen biyu su hada kansu don tabbatar da nasarar gudanar da harkokin "Shekarar Ilimi ta Sin da Rasha", tare da karfafa mu'amala tsakanin al'ummomin kasashen biyu, a fannoni irin su yawon bude ido, da al'adu, da matasa, da kafofin watsa labarai da dai sauransu, ta yadda za a fadada hadin gwiwa a tsakanin kananan hukumomi ko yankuna na kasashen biyu, da inganta tuntubar juna kan al'amuran dake shafar bangarori da dama, domin cimma sakamako na zahiri. Bayan taron, firaministocin kasashen biyu sun sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, ta taron ganawar firaministocin Sin da Rasha karo na 31. Haka kuma, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, wadanda suka shafi harkokin tattalin arziki da ciniki, da ayyukan sararin samaniya, da kimiyya da fasaha, da kuma aikin ba da ilimi da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Kasar Sin ta kaddamar da harba roka daga saman teku da ke kusa da birnin Rizhao na lardin Shandong da...
Ranar 22 ga watan Oktoba ita ce ranar maganin gargajiya ta duniya. Bayanai daga taron kasa da kasa karo na 23 kan maganin gargajiya na kasar Sin, wanda aka kammala kwanan nan sun nuna cewa, likitanci da maganin gargajiya na Sin ya yadu zuwa kasashe da yankuna 196, kuma adadin mutanen da suka samu jiyyar allurar gargajiya ta Sin, da tausa, da sauran fasahohin likitancin gargajiya na Sin a duniya ya wuce kashi daya bisa uku na jimillar al'ummar duniya, inda al'ummar kasashe da yankuna da yawa ke amfana da likitancin gargajiya na Sin. Hakika, likitancin gargajiya na Sin na yaduwa zuwa Afirka ta hanyoyi daban-daban, kuma yana shiga cikin tsarin kiwon lafiya na sassan nahiyar. A Mali, cibiyar Luban ta koyar da fasahar likitancin gargajiya na Sin ta riga ta yi aiki na sama da shekaru 6. A shekarar 2019, makarantar koyon aikin likita ta Tianjin ta yi hadin gwiwa da jami'ar kimiyya da fasaha ta Bamako dake kasar Mali, inda suka kafa cibiyar Luban ta farko ta koyar da fasahar likitancin gargajiya na Sin a duniya. Ya zuwa shekarar 2026, cibiyar ta horar da kwararru masu alaka da likitancin gargajiya na Sin sama da mutum dubu daya, daga cikinsu dalibai 54 sun zama kwararrun likitocin gargajiya na Sin bayan sun sami cikakken horo. Diarra Boubacar mutum ne da ya yi kira da a kafa wannan cibiyar, kuma shi kansa ya ganewa idonsa tarihin bunkasar cibiyar. Ya zo nan kasar Sin domin karatu a shekarar 1984, inda ya zama bakon farko da ya sami digiri na uku a fannin likitancin gargajiya na Sin. Daga nan, ya dade yana aikin likita a Sin, kuma a shekarar 2019 ya ingiza gina cibiyar Luban ta Mali. Ya ce, "Likitancin gargajiya na Sin gada ce da ke hada al'adu daban-daban. A nan gaba, za mu yi kokari wajen horar da tarin kwararrun likitocin gargajiya na Sin a cikin gidanmu, domin kara bunkasa likitancin gargajiya na Sin a Mali." A Harare babban birnin Zimbabwe kuwa, cibiyar likitancin gargajiya ta tsakanin Sin da Zimbabwe, tun kafuwarta a shekarar 2020, ta riga ta ba da hidimomin jinya, da magani sama da sau dubu 25, kuma ita ce cibiyar likitancin gargajiya ta Sin mafi girma a yankin kudu da Sahara na Afirka. Cibiyar ta yi hadin gwiwa da sashen kiwon lafiya na Zimbabwe, tana zabar dalibai masu hazaka zuwa cibiyar domin samun horo na gudanar da aikin likita a asibiti. A halin yanzu, dalibai da dama sun ci jarrabawa, wadanda suke iya gudanar da jinyar allura da kansu. Dalibi mai suna Richard Mutingwende, bayan ya ci jarrabawar, ya bude wani asibiti na likitancin gargajiya na Sin a Harare. Cibiyar likitanci da allurar gargajiya ta Sin ta Afirka, ita ce cibiyar horo ta gudanar da aikin jinyar allura ta jami'ar Johannesburg ta Afirka ta kudu. Tun daga shekarar 2020, jami'ar Johannesburg ta bude kwasa-kwasan allurar, inda kowace shekara take karbar kusan dalibai masu karatun digiri na farko kimanin 50, da daliban digiri na biyu 20, tana amfani da hanyar hada koyarwa a aji da aikin ba da jinya a asibiti tare, domin horar da kwararrun likitocin gargajiya na Sin. Har ila yau, a cikin azuzuwan jami'o'in likitancin gargajiya na Sin da dama dake Sin, dalibai daga Afirka har yanzu suna maimaita gwajin yadda za a yi jinyar allura a kan samfurin jiki. Wasu daga cikinsu, bayan sun kammala karatu sun koma gida, za su bude asibiti kamar yadda Diarra ya yi, ko kuma su zama likitocin farko da suka iya allurar a yankinsu kamar Richard. Likitancin gargajiya na Sin mahada ce tsakanin Sin da Afirka—daga Mali zuwa Harare zuwa Johannesburg—ya yadu zuwa Afirka bisa kokarin mutanen nahiyar, wadanda suka kai fasahar zuwa kasashensu, ta wannan mataki kuma ake fadada hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka. (Marubuciya: MINA)
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da wani taron manema labarai a yau Laraba, inda ya bayyana halin da kasar ke ciki wajen magance sauyin yanayi. Li Gao, mataimakin daraktan ma’aikatar kare muhalli da yanayi ta kasar, ya yi bayani a gun taron cewa, Sin ta dade tana bin hanyar samun ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, kuma ta samu manyan nasarori wajen magance sauyin yanayi. A cewar bayanin, a rabin farko na bana, karfin na’urorin samar da makamashin da ake iya sabuntawa na duk kasar ya kai kilowatt duk sa’a biliyan 2.455, wanda ya zama kashi 60.7% na dukkan karfin samar da wutar lantarki na kasar. A karshen watan Yuli, karfin samar da wutar lantarki ta hasken rana ya wuce na kwal a tarihi, ya zama babbar hanyar samar da wutar lantarki mafi girma. A halin yanzu, yawan na’urorin samar da wutar lantarki masu amfani da makamashin nukiliya da Sin ke aiki da su da wadanda aka amince a gina su, ya zama matsayi na farko a duniya, adadin kerawa da sayar da motoci masu aiki da wutar lantarki ya ci gaba da zama na farko a duniya cikin shekaru 11 a jere, ban da wannan kuma kasar ta gina cikakken tsarin samar da makamashi mai tsafta mafi girma a duniya, kana masana’antu masu tasowa da ayyukansu ba sa gurbata muhalli, sun zama muhimmin karfin ci gaban tattalin arziki. Kazalika, Li Gao ya ce, a lokacin “shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15”, ma’aikatar kare muhalli da yanayi za ta hada karfi da sauran sassan da abin ya shafa, don hanzarta ingiza samun ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma cika alkawarin da Sin ta yi a cikin yarjejerniyar Paris nan da shekarar 2030 a kan lokaci, game da taka rawar gani wajen magance sauyin yanayi gwargwadon karfinta. Bugu da kari, Li Gao ya ce, Sin tana bin ra’ayin kafa kyakkyawar makomar al’ummar bil’adama ta bai daya, kuma ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna guda 60 na hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan magance sauyin yanayi tare da kasashe masu tasowa 46, wanda hakan ya bayyana yadda take sauke nauyin dake wuyanta a matsayin babbar kasa. (Amina Xu)
Firaministan kasar Sin ya ce, a shirye suke su yi aiki da Rasha, tare da kara saka himma wajen jagorantar...
A bana ake cika shekaru 90 da cimma nasarar Doguwar Tafiya ta jar rundunar sojojin kasar Sin. Kuma a kwanan baya, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin neman bunkasa, inda ta bayyana kokarin da kasar Sin ta yi ta fuskar gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya, da kuma gudanar da shawarar Ziri daya da hanya daya cikin hadin gwiwa, a matsayin wata "Sabuwar Doguwar Tafiya". Dangane da wannan tsokaci, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, babban ruhin "Doguwar Tafiya" ya zaburar da al'ummar kasar Sin, tare da karfafa musu gwiwar shawo kan matsaloli da kalubaloli, wanda hakan ya haifar da nasarorin kasar Sin a fannin neman ci gaba na a-zo-a-gani. A halin yanzu, da ake kan sabuwar "Doguwar Tafiya" zuwa ga farfadowar al'ummar kasar Sin, kasar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, kan manufar diflomasiyya mai zaman lafiya da dogaro da kai, kana, za ta yi aiki tare da dukkan kasashe, ciki har da kasar Rasha, domin inganta zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da su, wajen gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya. Haka kuma, yau Talata, wato ranar 20 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekara daya da kafuwar hukumar shiga tsakani ta duniya wato IOMed. Dangane da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, tun bayan kafuwarta shekara guda da ta gabata, hukumar ta samu goyon baya mai yawa, da kuma karbuwa daga kasashen duniya, inda adadin kasashen da suka shiga hukumar ya karu zuwa 48. Haka zalika, ta yi nasarar shiga tsakani wajen sasanta takaddamar kasuwanci ta kasa da kasa, lamarin da ya sa ta samu yabo matuka, daga bangarorin da abin ya shafa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Kakakin majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa Mohammed Ahmed Al-Yamahi, ya yaba da muhimman kaidoji hudu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da shigar sassa masu ruwa da tsaki cikin ayyukan warware manyan batutuwan dake addabar kasashen Afirka. Al-Yamahi, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ya ce kaidojin na shugaba Xi, sun kafa muhimmin tsari don inganta warware tashe-tashen hankula ta hanyar siyasa cikin lumana, da mara baya ga zaman lafiya da daidaito, da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da taimakawa wajen ingiza samar da tsaro, da daidaito a matakin shiyyoyi da na kasa da kasa. Jamiin, ya kara da cewa kaidojin hudu, sun samar da ginshiki mai karfi na inganta hadin gwiwa, da goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa, da ingiza kokarin shawo kan kalubalen bai daya, da yayata adalci da karin daidaiton odar kasa da kasa. A ranar 13 ga watan Oktoban nan ne shugaba Xi ya gabatar da kaidojin hudu, yayin da yake ganawa a birnin Beijing da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. Kaidojin dai sun dace da bukatar amfani da jagorancin nahiyar Afirka, wajen warware batutuwa da dama, ciki har da wanzar da adalci da doka, da goyon bayan dakatar da tashe-tashen hankula domin samar da zaman lafiya, da magance sakamako da tushen matsalolin nahiyar. (Saminu Alhassan)
Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta sha bayyana adawarta da fakewa...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da rike ruhin jerin manyan shawarwarin da...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.