Kasar Sin ta kaddamar da harba roka daga saman teku da ke kusa da birnin Rizhao na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, inda ta shigar da sabon tauraron dan Adam zuwa zagayen da aka tsara.Rokar mai suna CERES-1 Y8 ta tashi sama a yau Laraba da misalin 11:39 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba roka ta Taiyuan, inda ya zama karo na 7 da aka harba rokar CERES-1 daga saman teku. (Suleiman Suleiman)
ADVERTISEMENT














