Likitancin Gargajiya Na Sin Ya Inganta Hadin Gwiwar Lafiya Tsakanin Sin Da Afirka
Ranar 22 ga watan Oktoba ita ce ranar maganin gargajiya ta duniya. Bayanai daga taron kasa da kasa karo na 23 kan maganin gargajiya na kasar Sin, wanda aka kammala kwanan nan sun nuna cewa, likitanci da maganin gargajiya na Sin ya yadu zuwa kasashe da yankuna 196, kuma adadin mutanen da suka samu jiyyar allurar gargajiya ta Sin, da tausa, da sauran fasahohin likitancin gargajiya na Sin a duniya ya wuce kashi daya bisa uku na jimillar al'ummar duniya, inda al'ummar kasashe da yankuna da yawa ke amfana da likitancin gargajiya na Sin. Hakika, likitancin gargajiya na Sin na yaduwa zuwa Afirka ta hanyoyi daban-daban, kuma yana shiga cikin tsarin kiwon lafiya na sassan nahiyar. A Mali, cibiyar Luban ta koyar da fasahar likitancin gargajiya na Sin ta riga ta yi aiki na sama da shekaru 6. A shekarar 2019, makarantar koyon aikin likita ta Tianjin ta yi hadin gwiwa da jami'ar kimiyya da fasaha ta Bamako dake kasar Mali, inda suka kafa cibiyar Luban ta farko ta koyar da fasahar likitancin gargajiya na Sin a duniya. Ya zuwa shekarar 2026, cibiyar ta horar da kwararru masu alaka da likitancin gargajiya na Sin sama da mutum dubu daya, daga cikinsu dalibai 54 sun zama kwararrun likitocin gargajiya na Sin bayan sun sami cikakken horo. Diarra Boubacar mutum ne da ya yi kira da a kafa wannan cibiyar, kuma shi kansa ya ganewa idonsa tarihin bunkasar cibiyar. Ya zo nan kasar Sin domin karatu a shekarar 1984, inda ya zama bakon farko da ya sami digiri na uku a fannin likitancin gargajiya na Sin. Daga nan, ya dade yana aikin likita a Sin, kuma a shekarar 2019 ya ingiza gina cibiyar Luban ta Mali. Ya ce, "Likitancin gargajiya na Sin gada ce da ke hada al'adu daban-daban. A nan gaba, za mu yi kokari wajen horar da tarin kwararrun likitocin gargajiya na Sin a cikin gidanmu, domin kara bunkasa likitancin gargajiya na Sin a Mali." A Harare babban birnin Zimbabwe kuwa, cibiyar likitancin gargajiya ta tsakanin Sin da Zimbabwe, tun kafuwarta a shekarar 2020, ta riga ta ba da hidimomin jinya, da magani sama da sau dubu 25, kuma ita ce cibiyar likitancin gargajiya ta Sin mafi girma a yankin kudu da Sahara na Afirka. Cibiyar ta yi hadin gwiwa da sashen kiwon lafiya na Zimbabwe, tana zabar dalibai masu hazaka zuwa cibiyar domin samun horo na gudanar da aikin likita a asibiti. A halin yanzu, dalibai da dama sun ci jarrabawa, wadanda suke iya gudanar da jinyar allura da kansu. Dalibi mai suna Richard Mutingwende, bayan ya ci jarrabawar, ya bude wani asibiti na likitancin gargajiya na Sin a Harare. Cibiyar likitanci da allurar gargajiya ta Sin ta Afirka, ita ce cibiyar horo ta gudanar da aikin jinyar allura ta jami'ar Johannesburg ta Afirka ta kudu. Tun daga shekarar 2020, jami'ar Johannesburg ta bude kwasa-kwasan allurar, inda kowace shekara take karbar kusan dalibai masu karatun digiri na farko kimanin 50, da daliban digiri na biyu 20, tana amfani da hanyar hada koyarwa a aji da aikin ba da jinya a asibiti tare, domin horar da kwararrun likitocin gargajiya na Sin. Har ila yau, a cikin azuzuwan jami'o'in likitancin gargajiya na Sin da dama dake Sin, dalibai daga Afirka har yanzu suna maimaita gwajin yadda za a yi jinyar allura a kan samfurin jiki. Wasu daga cikinsu, bayan sun kammala karatu sun koma gida, za su bude asibiti kamar yadda Diarra ya yi, ko kuma su zama likitocin farko da suka iya allurar a yankinsu kamar Richard. Likitancin gargajiya na Sin mahada ce tsakanin Sin da Afirka—daga Mali zuwa Harare zuwa Johannesburg—ya yadu zuwa Afirka bisa kokarin mutanen nahiyar, wadanda suka kai fasahar zuwa kasashensu, ta wannan mataki kuma ake fadada hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka. (Marubuciya: MINA)



















