Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako don taya cibiyar horar da ra’ayin gurguzu ta Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa.
Cikin wasikar, Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli ta sojin kasar, ya yaba wa cibiyar bisa horar da adadi mai yawa na wadanda ba ‘yan JKS ba, wadada suke da akidu irin na jam’iyyar, kuma suke aiki tare da ita cikin hadin gwiwa domin cimma burikan kasar. Ya kuma yaba da yadda cibiyar ta bayar da muhimman gudunmuwa wajen karfafa kishin kasa da hadin kai cikin shekaru 70 da suka gabata.
Haka kuma, shugaba Xi ya karfafa wa cibiyar gwiwar ci gaba da karfafa horon siyasa da samar da daidaito kan harkokin siyasa daban-daban da kuma kara ingancin ayyukan koyarwa da bincike da karfinta na tafiyar da harkoki. (Fa’iza Mustapha)














