Firaministan Sin Ya Ce Za A Karfafa Tabbatacciyar Alakar Hadin Gwiwa Mai Zurfi Tsakanin Sin Da Rasha
Firaministan kasar Sin ya ce, a shirye suke su yi aiki da Rasha, tare da kara saka himma wajen jagorantar...
Firaministan kasar Sin ya ce, a shirye suke su yi aiki da Rasha, tare da kara saka himma wajen jagorantar...
A bana ake cika shekaru 90 da cimma nasarar Doguwar Tafiya ta jar rundunar sojojin kasar Sin. Kuma a kwanan baya, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin neman bunkasa, inda ta bayyana kokarin da kasar Sin ta yi ta fuskar gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya, da kuma gudanar da shawarar Ziri daya da hanya daya cikin hadin gwiwa, a matsayin wata "Sabuwar Doguwar Tafiya". Dangane da wannan tsokaci, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, babban ruhin "Doguwar Tafiya" ya zaburar da al'ummar kasar Sin, tare da karfafa musu gwiwar shawo kan matsaloli da kalubaloli, wanda hakan ya haifar da nasarorin kasar Sin a fannin neman ci gaba na a-zo-a-gani. A halin yanzu, da ake kan sabuwar "Doguwar Tafiya" zuwa ga farfadowar al'ummar kasar Sin, kasar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, kan manufar diflomasiyya mai zaman lafiya da dogaro da kai, kana, za ta yi aiki tare da dukkan kasashe, ciki har da kasar Rasha, domin inganta zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da su, wajen gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya. Haka kuma, yau Talata, wato ranar 20 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekara daya da kafuwar hukumar shiga tsakani ta duniya wato IOMed. Dangane da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, tun bayan kafuwarta shekara guda da ta gabata, hukumar ta samu goyon baya mai yawa, da kuma karbuwa daga kasashen duniya, inda adadin kasashen da suka shiga hukumar ya karu zuwa 48. Haka zalika, ta yi nasarar shiga tsakani wajen sasanta takaddamar kasuwanci ta kasa da kasa, lamarin da ya sa ta samu yabo matuka, daga bangarorin da abin ya shafa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Kakakin majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa Mohammed Ahmed Al-Yamahi, ya yaba da muhimman kaidoji hudu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da shigar sassa masu ruwa da tsaki cikin ayyukan warware manyan batutuwan dake addabar kasashen Afirka. Al-Yamahi, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ya ce kaidojin na shugaba Xi, sun kafa muhimmin tsari don inganta warware tashe-tashen hankula ta hanyar siyasa cikin lumana, da mara baya ga zaman lafiya da daidaito, da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da taimakawa wajen ingiza samar da tsaro, da daidaito a matakin shiyyoyi da na kasa da kasa. Jamiin, ya kara da cewa kaidojin hudu, sun samar da ginshiki mai karfi na inganta hadin gwiwa, da goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa, da ingiza kokarin shawo kan kalubalen bai daya, da yayata adalci da karin daidaiton odar kasa da kasa. A ranar 13 ga watan Oktoban nan ne shugaba Xi ya gabatar da kaidojin hudu, yayin da yake ganawa a birnin Beijing da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. Kaidojin dai sun dace da bukatar amfani da jagorancin nahiyar Afirka, wajen warware batutuwa da dama, ciki har da wanzar da adalci da doka, da goyon bayan dakatar da tashe-tashen hankula domin samar da zaman lafiya, da magance sakamako da tushen matsalolin nahiyar. (Saminu Alhassan)
Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta sha bayyana adawarta da fakewa...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da rike ruhin jerin manyan shawarwarin da...
A yau Talata a birnin Nanjing, an gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar “shirin karfafa manyan kamfanoni” tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da gwamnatin lardin Jiangsu, kana an gabatar da jerin ayyukan yada labarai na hadin gwiwa. Shen Haixiong, shugaban CMG ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. A jawabinsa Mr. Shen ya ce, a matsayin babban rukuni mafi girma, kuma mafi nau’ikan ayyuka da yada labarai ga wurare mafi yawa a duniya a yau, “shirin karfafa manyan kamfanoni” na CMG na ci gaba da karfafa wa manyan kamfanonin Sin gwiwa don su zama sahun gaba da fadada tasirinsu a duniya. Ya ce CMG zai ci gaba da yada labaran da suka shafi Jiangsu, da kara hadin gwiwa wajen karfafa wa manyan kamfanonin gwiwa, da zurfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire tsakanin gwamnatin tsakiya da mabambantan wurare na kasar, kana da amfani da hanyoyin kirkire-kirkire wajen taimaka wa manyan kamfanonin Jiangsu yada tasirinsu ba iyaka. Haka zalika a yau din, an gudanar da taron “fafatawar fasaha: babban baje kolin fasahar amfani da na’urorin mutum-mutumin inji, karo na farko” na CMG, zangon Nanjing. (Amina Xu)
Kai Ziyara “Haikalin Masu Laifin Yaki” Da ’Yan Siyasar Japan Suka Yi Yunkuri Ne Na Farfado Da Ra’ayin Fin Karfin Soja Firaministan Japan Sanae Takaichi ta ziyarci “Haikalin masu laifin yaki” tare da ba da hadaya da kudaden hadaya a ranekun 17 da 19 ga watan Oktoba. Bugu da kari, wasu jami’an majalisar gudanarwa ta Japan da manyan jami’an jam’iyyar Liberal Democratic Party da dama su ma sun ziyarci haikalin. Wannan ya bayyana yunkurinsu na gyara zalunci da mamaya da masu aikata laifin yaki na Japan suka yi a yakin duniya na biyu, da nufin “farfado da ra’ayin fin karfin soja”. A shekarar 1978, masu ra’ayin rikau na Japan suka shigar da kaburburan masu laifin yakin duniya na biyu cikin sirri a haikalin Yasukuni inda ake kiran shi “Haikalin masu laifin yaki” a halin yanzu. Sanae Takaichi ta yi wa haikalin lakabin “haikalin zaman lafiya” a fili, kuma cikin kusan shekaru 20 da suka gabata, a kusan kowace shekara tana tunawa da wadannan masu aikata laifin yaki, da nufin musanta hukuncin da kasashen duniya suka yi wa Japan a tarihi a kotun Tokyo, da kalubalantar adalci da gaskiyar kasa da kasa da da’ar bil’adama. Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, masu ra’ayin rikau na Japan sun kara daukar matakan jirkita tarihi, wanda ke da mugun nufi na hanzarta “farfado da ra’ayin fin karfin soja”. Game da ayyukan da masu ra’ayin rikau na Japan ke yi na kalubalantar tsarin duniya bayan yakin duniya na biyu da farfado da ra'ayin fin karfin soja, Sin da sauran kasashen da aka zalunta a yakin duniya na biyu ba za su yi shiru ba. Idan wasu daga cikin Japanawa suna nufin bin tsohuwar hanyar mamaya da fadada da zalunci, to tabbas za a yi musu cikakken hukunci da martani. (Amina Xu) Kai Ziyara “Haikalin Masu Laifin Yaki” Da ’Yan Siyasar Japan Suka Yi Yunkuri Ne Na Farfado...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako don taya cibiyar horar da ra’ayin gurguzu ta Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa. Cikin wasikar, Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli ta sojin kasar, ya yaba wa cibiyar bisa horar da adadi mai yawa na wadanda ba 'yan JKS ba, wadada suke da akidu irin na jam'iyyar, kuma suke aiki tare da ita cikin hadin gwiwa domin cimma burikan kasar. Ya kuma yaba da yadda cibiyar ta bayar da muhimman gudunmuwa wajen karfafa kishin kasa da hadin kai cikin shekaru 70 da suka gabata. Haka kuma, shugaba Xi ya karfafa wa cibiyar gwiwar ci gaba da karfafa horon siyasa da samar da daidaito kan harkokin siyasa daban-daban da kuma kara ingancin ayyukan koyarwa da bincike da karfinta na tafiyar da harkoki. (Fa’iza Mustapha)
Bisa lissafi na farko-farko, alkaluman GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 10.71071 a rubu’i 3 na farkon bana, inda aka samu karuwar kaso 4.6 a mizanin shekara-shekara. Kafofin yada labarai na kasa da kasa kamar BBC da Reuters, sun gabatar da nasu sharhi masu take daban-daban kamar “Tattalin Arzikin Sin ya Karu a Q1-Q3” da “Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin daga Q1-Q3 ya Wuce Tsammani”… Bisa kididdiga, gudunmuwar da manyan masana’antu na kasar suka bayar ga tattalin arzikin ya karu da kaso 5.3 cikin rubu’i 3 na bana, yayin da sayayyar kayayyaki da na hidimomi ta karu da kaso 2.6. Galibin ma’aunan tattalin arziki sun samu ci gaba, lamarin da ke nuna juriya da kuzarin habakar tattalin arzikin Sin da ma jaddada matsayinsa na mai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya ga kasashe da yankuna 169, inda jimilar kayayyakin da ke shiga kasar da ma wadanda ke fita ta karu da kaso 18.8 a mizanin shekara-shekara cikin rubu’in 3. Baya ga haka, karuwar kayayyakin da kasar Sin take saya daga ketare ta ci gaba da zarce kaso 20 cikin dukkan rubu’in 3, wadda ke kara nuna matsayin Sin na babbar mai saye da sayarwa. Yanzu haka, yanayin duniya na cike da sarkakiya da sauye-sauye, kuma tubalin ingantuwar tattalin arzikin Sin yana bukatar karin karfi. Sai dai ya kamata a lura cewa, abubuwan dake ingiza ci gaba mai inganci a kasar na ci gaba da karuwa, lamarin da ke samar da goyon baya mai karfi ga burin kasar na samun karuwar tattalin arzikinta. (Fa’iza Mustapha)
Kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani a ranar Asabar, wadda ta ce a shekarun baya-bayan nan, tsarin ilimin sana’o’i na kasar, yana samar da matsakaicin adadi na kwararrun ma’aikata miliyan 10 ga masana’antu daban-daban a duk shekara. Mun saba da jin “in dambu ya yi yawa ba ya jin mai” a matsayin dalili ko kuma hanyar lullube gazawar wani tsari. Tabbas ina da yakinin mutane da dama kamar ni, sun amince da hakan. Sai dai, zamana a kasar Sin da abubuwan da na shaida, sun fahimtar da ni cewa, “duk yawan dambu zai ji mai, sai dai in ba a zuba isasshe ba.” Kuma “yawan dambu” ba matsala ba ce, maimakon haka, hanya ce ta samun arziki da dogaro da kai. “Dambu” a nan na nufin jama’a. A kasar Sin ne na ga yadda yawan jama’a ya zama alheri da hanyar samun wadata da dogaro da kai. Maimakon yawan jama’a ya zama tasgaro ga ci gaban kasar, sai ya zama karfin da ke ingiza ci gaba da wadata da kwanciyar hankalinta. Rashin aikin yi na zama babban dalilin dake haifar da talauci da aikata laifuffuka kamar sace-sace da fashi da makami, da tashe-tashen hankula da ake samu a cikin kasa. Sanin hakan ne ya sa kasar Sin tashi tsaye wajen bunkasa samar da ilimin fasahohi da sana’o’in hannu, domin samar da guraben aikin yi da kwararru, wanda zuwa yanzu ya kara karkata ga inganta kwarewa da biyan bukatun da masana’antun kasar ke da su. Kasar Sin na da kimanin makarantun koyar da sana’o’i sama da 10,000 da suka hada da na matakin sakandare da na gaba da sakandare, wadanda ke da dalibai sama da 30,000. Wannan mataki ya ba yara da matasa damar gano basirar da suke da ita, da bayar da gudunmawa ga cimma burikansu. Haka kuma, wata hanya ce ta ba dalibai samun kwarin gwiwa, domin za su samu bangarorin da suka fi sha’awa da basira a kai don raya su. Wannan ya saba da tsarin nan na lallai sai an yi karatu kan wasu takaitattun fannoni da watakila dalibi ba shi da sha’awarsu. Mutane sun bambanta, watau yayin da wani ke son karatun zube, wani kwarewarsa na ga bangaren abubuwan da zai iya yi da hannayensa. Wannan tsari na Sin yana ba da gudunmawa ga ci gaban kasa ta hanyoyi daban-daban, daga rage zaman kashe wando da aikata laifuka, zuwa biyan bukatun kasa da zama mai dogaro da kai da samar da al’umma mai ilimi da yaki da talauci da sauransu. Kuma shi ya ba kasar damar zama na daya a duniya a bangarori daban daban. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta lashe gasar nuna kwarewar aiki ta kasa da kasa da aka yi a baya-bayan nan a birnin Shanghai a karo na 5 a jere, inda ta mamaye teburin lambobin yabo, ta lashe lambobin zinare 41 da azurfa 11 sai tagulla 4 da kuma lambobin yabo na kwarewa guda 6. Hakika duk kasar da ta jajirce wajen wadata al’ummarta da ilimi daidai gwargado, ta ba matasanta damar nakaltar sana’o’i, to ta yi nisa a tafarkin ci gaba mai inganci, kuma ba makawa, ta tabbatar da tsara kyakkyawar makomarta. (Faeza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.