Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa
Yayin da yanayin duniya ke cike da sauye-sauye da tashe-tashen hankali, gibin tsaro na kara haifar da damuwa. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, ya nuna kaso 89.6 na masu bayar da amsa na kira ga dukkan kasashe su warware takkadama a tsakanin su ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa. Yayin da kaso 80.4 na masu bayar da amsa daga kasashe masu tasowa suka bayyana cewa, dabi’ar yakin cacar baka da neman iko, na barazana ga zaman lafiya a duniya da kara kalubalen tsaro, suna masu kira ga dukkan kasashe su hada hannu wajen samar da tsarin tsaro mai inganci da daidaito da dorewa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)



















