Fasahar kirkirarriyar basira ta AI na ci gaba da fita daga dakunan bincike cikin sauri, tana shiga masana’antu, harkokin sufuri, tsarin kudi da sauran fannoni na rayuwar yau da kullum. Kuma a yayin da gasar kasashe kan bunkasa manyan fasahohin AI ke kara zafafa, wata muhimmiyar tambaya na kara tasowa: wace kasa ce za ta shimfida fukafukanta ga kasashe masu tasowa ta yadda ba wai kawai ta taimake su da fasahar ba, har ma da hanyar amfani da ita wajen magance matsalolin tattalin arzikinsu?
Tuni dai kasar Sin ta nuna muradinta na bayar da wannan taimako a wurare da tarurruka daban-daban, inda ta kuduri aniyar agazawa tare da kulla hadin gwiwa da kasashe ta fuskar ba da horaswa da kafa cibiyoyi da kuma fadada amfani da AI wajen zamanantar da masana’antu.Ko a kwanan nan, Sin ta jaddada buƙatar kirkiro da wani tsari na fasahar AI da zai kasance mai bude kofa ga kowa da yin hadin gwiwa, da karfafa bincike kan manyan samfuran AI na harshe, da samar da shirye-shiryen ba da horo da kayayyakin aiki na fasahar zamani da za su ba kasashe masu tasowa damar more wannan sabon ci gaban tattalin arzikin cikin sauki.
Daya daga cikin misalan da za a iya ganin haka a aikace shi ne taron dandalin kasuwancin Dubai da kasar Sin da zai gudana a ranar 14 ga watan Oktoba mai kamawa, inda ake sa ran shugabannin kasuwanci daga Dubai da Sin za su tattauna hanyoyin fadada kasuwanci, da zuba jari da hadin gwiwa a fannoni kamar tattalin arzikin fasahar zamani, da sufuri da masana’antu masu aiki da fasahohin zamani. Kazalika, Sin ta tsara shirye-shiryen horar da kwararrun Afirka a fannonin AI, da tsaron shafin intanet, da fannonin da aka dunkule cikin sunan STEM, watau kimiyya, da fasaha, da injiniyanci da kuma lissafi, har ma a karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, an yi tanadin horar da kwararrun Afirka 1,000 a fannonin kimiyya da fasaha, tare da shirye-shiryen horar da malamai da ma’aikatan fasaha a tsakanin shekarar 2025 zuwa ta 2027.
Kazalika, a Brazil, an ambaci amfani da tsarin binciken fasaha na kasar Sin wajen taimakawa tabbatar da daidaiton tsarin wutar lantarki. Wasu kasashen Asiya ma, suna amfana da fasahohin AI da Sin ta samar musu. Misali, a Pakistan, ana amfani da fasahohin Sin a fannin aikin gona, da tsaro, tare da horas da dalibai da kwararru a jami’o’i da cibiyoyin fasaha.
A Malaysia, kamfanonin Sin suna taimakawa wajen gina birane na fasahar zamani, da amfani da AI a masana’antu, da sauransu. Haka lamarin yake ma a Indonesia, Thailand, Singapore da Cambodia wadanda duk suna cin gajiyar wadannan fasahohin zamani daga kasar Sin.
Bugu da kari, wani abin sha’awa ga wannan muradi na Sin na raba fasahohin zamani ga kasashe masu tasowa shi ne, ba wai kawai tana ba su fasahohin ne don nuna cewa su ma suna da su ba ne kawai, har ila yau tana hadawa ne da tsarin da zai taimaka wa kasashen wajen bunkasa ayyukansu, da rage kudin samarwa, da kuma samar da sabbin hanyoyin samun ci gaba. Hakika dai, masu iya magana kan ce, “hakika mai bayarwa ba ya rasawa”. Bisa wannan kyakkyawar kuduri na kasar Sin na taimakawa saura, ita ma za ta ci gaba da ganin budi daga dukkanin fannoni na ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














