Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya ƙarfafa gwiwar ’yan Nijeriya su saka hannun jari a Matatar Dangote da ke gudana a halin yanzu.
Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, yana mai cewa ’yan Nijeriya da ke cikin gida da ƙasashen waje sun nemi jin ra’ayinsa kan batun sayen hannun jarin matatar mai ta Dangote da darajarsa ta kai Naira tiriliyan 2.15.
Obi ya ce ya ƙarfafa su su sayi hannayen jarin, yana mai bayyana jin daɗinsa kan jarin da Alhaji Aliko Dangote ya zuba a ɓangaren masana’antu da sauran fannoni na tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce, wannan shirin na matatar ya ƙara tabbatar da matsayinsa na cewa Nijeriya na buƙatar sauya tattalin arzikinta daga dogaro da shigo da kayayyaki zuwa samar da kayayyaki a cikin gida.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya kuma yi kira ga ’yan kasuwar Nijeriya da su ƙara saka jari a ɓangarorin da ke samar da kayayyaki da ayyuka, tare da bai wa ’yan ƙasa damar mallakar kaso a kamfanoni ta hanyar sayar da hannayen jari ga jama’a.














