Khalid Idris Doya" />

Ayyuka: Jihar Filato Ta Amince Da Fitar Da Biliyan Uku Daga Yarjejeniyar Zuba Jari

Sassauta Dokar Hana Fita

Majalisar Zartaswar jihar Filato ta amince da fitar da naira biliyan uku (N3b) daga asusun ajiyar yarjejeniyar zuba jarin babban kasuwa domin gudanar da wasu manyan ayyukan raya jihar.

Wannan matakin na zuwa ne bayan zaman da majalisar ta yi a 2021 a ranar Juma’a karkashin jagorancin gwamnan jihar Simon Bako Lalong da ya gudana a gidan gwamnatin jihar ta Little Rayfied, Jos.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Mista Dan Manjang; kwamishinan kudi na jihar, Dakta Misis Regina Soemlat da kuma kwamishinan kasuwanci da masana’antu, Misis Abe Aku su ne suka bada wannan bayanin na matsayar da suka dauka yayin da suke tsegunta wa ‘yan jarida kadan daga cikin matakan da zaman da suka aiwatar ya cimma.
Kwamishinan yada labaran, Dan Manjang, ya yi bayanin cewa amincewa da fitar da kudaden zai taimaka sosai wajen ganin an samu nasarar karasa wasu daga cikin muhimman ayyukan raya jihar da ake kan gudanar da su a halin yanzu.
Ya ce, bisa raguwar kason kudaden shiga na haraji da kuma raguwar adadin kaso-kaso da ake amsa daga asusun gwamnatin tarayya sakamakon annobar Korona, hakan ya sanya gwamnatin jihar daukan matakan da suka dace wajen ganin an samu kudade ta wasu hanyoyin domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya jihar da al’umman jihar.
Ita kuma kwamishinan kudi na jihar, Dakta Misis Regina Soemlat cewa ta yi, biliyan uku din na daga cikin bari ne na adadin kudi yaryeyeniyar zuba jari ta naira biliyan 30 da aka samar tun da fari ta tsarin kafa tarihin gwamna mai ci ta fuskacin zuba ayyukan raya jihar wato ‘Lalong Legacy Projects’.
A cewarta hakan zai bada damar kammala shirin kafa tarihi na gwamna mai ci na samun nasarar kammala ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar a halin yanzu.

Exit mobile version