Masu ababen hawa da mazauna jihohin Arewa 14 da aka yi watsi da ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohinsu sun yi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ministan ayyuka, Injiniya Dabid Umahi, kan halin da suke ciki na kunci bisa tabarbarewar hanyoyin gwamnatin tarayya.
Wani bincike da LEADERSHIP ta gudanar a jihohin Arewa 19 ya nuna cewa an bayar da kwangilar ayyukan manyan tituna da aka yi watsi da su tun bayan gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Wasu kuma an yi watsi da ayyukan manyan titunan ne tun shekaru 10 da suka gabata na gwamnatocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wanda ya gaje shi, Muhammadu Buhari.
Sai dai Jihar Borno, wadda har zuwa lokacin hada wannan rahoto a daren jiya ba a samu kammala rahotonta ba, sauran jihohin da abin ya shafa an yi watsi da ayyukan tituna ne a tsakanin biyu zuwa 10.
Jihohi hudu da suka hada da Kaduna, Kebbi, Taraba, da Zamfara su ne mafi karancin hanyoyin da aka yi watsi da su, yayin da Jihar Kwara ke da mafi yawan ayyukan hanyoyin da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a karkashin jagorancin Tinubu.
A Jihar Katsina kuwa, akwai kananan titunan gwamnatin tarayya da ke cikin mawuyacin hali, inda mafi yawansu ke bukatar gyara cikin gaggawa.
Titin Katsina zuwa Kano, wadda gwamnatin da ta shude ta bayar ba a kammala ba, ta tsaya a Gidan Mutun Daya.
Titin Mararaba Kankara zuwa Kankara a halin yanzu ana kan gyarawa, amma sauran muhimman hanyoyin ko dai an kasa gyarawa ko kuma ‘yan ta’adda sun mamayesu, wanda hakan ke kawo hadarurruka.
Titin Funtua zuwa Sheme dai ya shafe tsawon lokaci yana a lalace, lamarin da ya ta’azzara matsalar sace-sacen mutane da ake yi a yankin.
Haka zalika, titin Dutsinma zuwa Kankara, duk da cewa ana kulawa da shi sosai, ya zama yankin da ke fuskantar hadari saboda ‘yan fashin suna yi wa masu ababen hawa kwanton bauna tare da kai su dajin Rugu.
A Jihar Zamfara, babbar hanyar Jibiya zuwa Kaura Namoda, wacce a ake ganin hanya ce mai kyau da ta hada jihohin Katsina da Zamfara, amma a yanzu ta zama tarkon mutuwa saboda yawaitar ‘yan fashin daji.
A shekarar 2020, gwamnatin jihar ta ayyana shi a matsayin yankin da ba za a iya bi ba, tare da hana masu ababen hawa yin amfani da hanyar saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.
A Jihar Neja, kusan dukkan titunan gwamnatin tarayya sun lalace, wasu kuma gwamnatin jihar ta karbe su.
An shafe sama da shekaru 10 ana aikin titin Suleja zuwa Minna, wanda dan kwangilar ya yi watsi da shi tsawon shekaru uku, kafin ya koma aiki kimanin shekaru biyu da suka wuce. Ko da yake, binciken LEADERSHIP ya nuna cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin gina sauran sassan hanyar da ta tashi daga Kakaki a karamar hukumar Paikoro zuwa Minna, babban birnin jihar, saboda tafiyar hawainiya da aikin hanyar yake yi.
Haka kuma bangaren Agaie-Bida na hanyar Lambata-Bida har yanzu yana cikin mummunan yanayi duk da cewa an bayar da kwangilolin hanyar kimanin shekaru biyar da suka gabata, haka ma hanyoyin Mokwa-Jebba, Mokwa-Bokani-Tegina da Minna-Tegina-Kontagora.
A kwanakin baya ma gwamnatin Jihar Neja ta karbe aikin titin Kontagora zuwa Rijau daga hannun gwamnatin tarayya, saboda dan kwangilar ya yi watsi da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama.
Haka zalika, titin Minna-Sarikin Pawa da gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta fara, an yi watsi da shi tsawon shekaru 20, yayin da ba a tabbatar ko an bayar da kwangilar aikin titin Mokwa-New Bussa, wanda yanzu ya lalace ba.
A Jihar Filato, titin Jos-Akwanga, Bauchi zuwa Gombe, da Panbegwa a Jihar Kaduna da ke bi ta hanyar Saminaka zuwa Jingir da Bom Manchok, da dai sauransu, titunan gwamnatin tarayya ne da aka dade da yin watsi da su, kuma suna bukatar dauki cikin gaggawa.
Bayan haka, hanyar dajin Hawan-Kibo zuwa Jos, duk da cewa ta samu wasu tsaiko a bara, amma akwai bukatar a kara hada karfi da karfe wajen gyarata, domin ita ce babbar hanyar da ta hada yankin arewa maso gabashin Nijeriya.
A halin yanzu, wadannan hanyoyi sun zama tarkon mutuwa ga matafiya, wanda suka kasance sassanin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, wadanda suka yi wa titunan kawanya, suna jiran masu ababen hawa da ba su ji ba gani su kai musu farmaki.
LEADERSHIP ta gano cewa an bai wa wasu kamfanonin gine-gine hudu kwangilar gyaran wadannan hanyoyi a watan Maris na 2020.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya kuma nuna cewa ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin gyaran wadannan hanyoyi sun bar wuraren, kuma masu ababen hawa na ci gaba da kokawa dangane da rashin kyawun hanyoyin.