Jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Garzali Miko, ya bayyana cewa babban burinsa bai wuce ya samu kuɗaɗe ta hanyar sana’arsa ta fina-finai a Kannywood ba.
Miko ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jarumar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta na ‘Gabon’s Room Talk Show’.
- Furodusoshin Kannywood Sun Yi Taron Kawo Gyara A Masana’antar
- Ban Yi Da Na Sanin Kalaman Da Na Furta Game Da Masana’antar Kannywood Ba -Amdaz
Da yake amsa tambaya akan aikin da ya fi so a tsakanin waka da fitowa a cikin Fim, Garzali Miko, ya bayyana cewar ya fi sha’awar waka.
Domin a waka aka san shi kuma a waka ya samu kuɗi, duk da yana sha’awar fitowa cikin fin amma ya fi sha’awarar waƙoƙi da rawa.