Jarumin Kannywood wanda a kwanakin baya ya fallasa wani boyayyen sirri kamar yada ya ce game da masana’antar shirya fina finan Hausa na Kannywood Abdullahi Amdaz.
Ya bayyana cewar har yanzu yana a kan bakansa dangane da maganar da ya yi a wata hira da yayi da jami’an hukumar Hizba ta jahar Kano.
- Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa
- Sharhi: Raunin Jam’iyyun Adawa Da Barazana Ga Dimokuradiyyar Nijeriya
Amdaz wanda yake ci gaba da shan suka daga wasu wadanda ke ganin abinda ya yi bai dace ba duba da cewar shima yana cikin sana’ar da yake ikirarin cewar tana bata tarbiyar yara.
A kwanakin baya Amdaz ya samu sammacen kotu a kan ya janye kalaman da ya yi a kan masu shirya fina finan Kannywood cikin sa’o’i 48 kuma ya fito fili ya basu hakuri.
Abinda ya kira da abu marar yiwuwa, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewar.
“Mun karbi kuma zamu bita da HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL.
Amma ina son ku sani daga yanzu har Mahdy ya bayyana a busa kaho, banga kotu ko wani Dan Adam daya isa ya saka na karyata kaina ba, ba awa 48 ba har zaren agogo ya tsinke, babu wanda ya isa ya sanyani bada hakuri a cikin hakkin Ubangijina ba.
Duk abinda na fada na fada bazan karyata kaina ba akan wannan maganar. Tunda kun kasa kawo hujja ko karyata abinda na fada, kawai ku karbi gaskiya ku huta, kuyi Umarni da kyakykyawa kuyi hani da mummuna.
Daga karshe dai tsohon dan kasuwar ya bayyana cewar a shirye yake ya tunkari shari’a kuma ya bada hujjoji domin wanke kanshi.